"Gudummawar marubuta wajen gyaran al'umma ba kaɗan ba ce" - Hajaru Baba Sakkwato

Daga Abba Abubakar Yakubu


Malama Hajaru Abdullahi Baba fitacciyar 'yar jarida ce da ke aiki a tashar rediyo ta Vision FM a garin Sakkwato Birnin Shaihu. Marubuciya ce da ta samu nasarar wallafa littafin ta na farko mai suna KISHIYAR MAFALKI kimanin shekaru goma da suka gabata, amma halayyar wasu' yan kasuwar littattafan Hausa marasa tausayi ya sa ta tsorata da harkar buga littafi, ta koma tunanin sake rubuce rubucen ta na gaba a yanar gizo wato online kawai.

Hajaru Baba Sakkwato


A tattaunawar ta da ABBA ABUBAKAR YAKUBU , marubuciyar wacce kuma har wa yau 'yar siyasa ce kuma 'yar kasuwa ta bayyana gudunmawar da harkar rubutun Adabi ke bayar wa ga ci gaban harkokin zamantakewa da shugabanci, da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin ta sauran marubutan Jihar Sakkwato. Ga yadda tattaunawar ta su ta kasance.


Download our app now


ADABI: Ko za ki gabatar mana da kan ki?


HAJARU: Sunana dai Hajaru Abdullahi Baba. Kuma ni haifaffiyar garin Sakkwato ce, a nan na tashi har na yi karatu na, yanzu kuma nake aiki a tashar rediyo ta Vision FM da ke nan Sakkwato, inda nake gabatar da labaru da shirye shirye, da kuma kasuwanci da nake gudanarwa.


ADABI: Wanne irin kasuwanci ki ke yi?


HAJARU: Ina gudanar da kasuwanci ne na kayan mata, na gyaran jiki da na aikace aikacen gida, tufafi da sauran su. Duk wani abu dai da za a ɗan samu riba ko yaya take, ina juyawa.


ADABI: Ko za ki iya bayyana mana wacce gudunmawa ki ke bayar wa a harkokin siyasa?


HAJARU: Alhamdulillah, gudunmawar da nake bayar wa a siyasa bai wuce ƙoƙarin da nake yi na ganin an tsaftace harkokin siyasa, a daina bangar siyasa, kuma a bai wa mata dama su ma su shiga a dama da su a bangaren siyasa, tare da ba su madafun iko, saboda irin gudunmawar da suke bayarwa ga siyasa. Domin mata da matasa su ne ƙashin bayan cigaban siyasa. Waɗannan na daga cikin muhimman abubuwan da suka fi ɗaukar hankalina a siyasa, kuma ko a cikin shirye shiryen da nake gabatarwa a gidan rediyo, ina ƙoƙarin faɗakar da jama'a masu sauraro a kai. Sannan a wani lokaci a baya na taɓa riƙe muƙamin mai bai wa Gwamna shawara, a gwamnatin da ta gabata, wato zangon farko na Mai Girma Aminu Waziri Tambuwal. 


ADABI: Ba ni labarin yadda ki ka fara sha'awar rubuce rubuce?

Hajaru Baba a ɗakin watsa shirye-shirye na Rediyo


HAJARU: Na fara sha'awar karatu da rubutu tun ina firamare, inda na fara karanta littafin Magana Jari Ce. Tun daga sannan na ji sha'awar karatun littattafan Hausa ya shige ni. Ba na mantawa lokacin ina makarantar sakandire idan mun dawo gida nake zama ina 'yan rubuce rubucena, sai dai ban taba tunani buga littafi ba, sai daga baya cikin shekarar 2011 na wallafa littafina na farko Kishiyar Mafalki. 


Sai dai daga kansa ban ƙara buga littafi ba saboda yadda dillalan littattafan Sakkwato suka riƙe mun kuɗi, kuma gaskiya hakan ya yi matuƙar sanyaya min gwiwa, domin kuwa tun daga lokacin ban sake wallafa wani littafi ba, duk kuwa da Ina da rubuce rubucen da dama a ƙasa. Amma yanzu tun da na lura da yadda hankalin masu karatu ya karkata ga karatun Online, nima na fara tunanin sake wasu rubutun da na yi a kafar sadarwa ta yanar gizo, wato online ɗin kenan.

Sauƙe manhajar Mujallar ADABI app ta wannan link

ADABI: Yaya ki ke ganin makomar harkar rubutu da ke komawa online a manhajar yanar gizo?


HAJARU: A gaskiya wani ɓangaren za mu iya cewa hakan tamkar mayar da darajar rubutu baya ce, kuma hakan na iya kashe harkar baki ɗaya, saboda bugawar yana da matuƙar muhimmanci. Kuma zai shiga tarihi, yaran mu da iyayen mu da sauran al'umma za su gani su karanta. 


Bambacinsa kenan da yanar gizo da sai kana da babbar waya da data. Ko da yake na lura yanzu marubuta sun fi son hakan saboda a nan suke sayar da littattafan su ba ruwansu da kaiwa kasuwa, ballantana a cinye musu kuɗi. Kuma ba su yi wahalar fitar da kuɗin bugawa ba, sannan a hakan kuma duniya ce ke ganin rubutun a ko'ina. Kana magana da su ka biya kuɗi su tura maka. ADABI: Wanne ƙalubale ki ka fuskanta a matsayin ki na marubuciya?


HAJARU: Ƙalubalen da na fuskanta bai wuci yadda waɗanda na kai wa littafan ke cinye min kuɗi su hana, alhalin kuwa ba littafin ba kudin, an sayar. Ni kuma saboda ba na son tashin hankali haka na bar su.


ADABI: Wacce gudunmawa marubuta ke bayarwa wajen kawo sauyi a rayuwar al'umma?


HAJARU: Alhamdulillah, marubuta suna bada gudunmawa sosai wajen kawo sauyi ga rayuwar al'umma a ɓangaren rubutu, saboda sune ke duba wani halin da al'umma ke ciki su yi rubutu a kai, kuma sai ka ga cikin ikon Allah saƙon su yana isa.


ADABI: Wanne irin goyon baya gwamnati da hukumomi za su bai wa marubuta domin yin rubuce rubuce na faɗakarwa da jan hankali game da tsare tsaren da ake buƙatar wayar da kan jama’a a kai?


HAJARU: Ya kamata hukumomi da gwamnatoci su shigo domin bayar da gudumuwarsu a kan sha'anin rubutu saboda gaskiya lamarin rubutu ba karamin abu ba ne ga ci gaban rayuwar al'umma, domin kuwa cikin hikima za su kawo gyara a kowane irin lamari, musamman abin da jama'a suke wahalar amincewa da shi, saboda rashin fahimta ko ƙarancin wayewa.


ADABI: Yaya za a kwaɗaitar da harkar rubuce rubuce a tsakanin ɗaliban makarantu, don bunƙasa harshen Hausa da harkar ilimi?HAJARU: Yana da kyau marubuta su riƙa yin rubutu mai mahimmanci da ya shafi zahirin rayuwa ta yau da gobe, tare da sanya hikima a cikin rubutun su, wanda shi zai kwaɗaitar da masu karatu da ɗalibai har su yi sha'awar su ma su gwada basirar su da kafa ƙungiyoyin marubuta a tsakanin su.


ADABI: Menene alaƙar ki da sauran marubuta na Jihar Sakkwato?


HAJARU: Alhamdulillah, muna haɗuwa muna kuma bai wa junan mu shawarwari da gudunmawa sosai tamkar tsintsiya madaurinki ɗaya muke. Kuma ana samun ci gaba sosai, sabbin marubuta na ƙara bayyana kansu.


ADABI: Menene burin ki na rayuwa a matsayin ki na marubuciya?


HAJARU: Burina a rubutu shi ne in ba da gudunmawa sosai ga al'umma wanda idan nayi rubutu zai taɓa rayuwar wasu musamman masu aikata wasu halaye marasa kyau, kuma ta dalilin rubutuna su gyara. Fatan mu a ko da yaushe mu ilimantar, mu faɗakar tare da ba da nishaɗi.


ADABI: An ce akwai wani ƙoƙari da ki ke yi a kafar sadarwa ta YouTube wanda shi ma ya shafi harkar Adabi, ko masu karatun mu za su sani?


HAJARU: E, haka ne. Ina da zaure a kafar YouTube mai suna TASKAR YUSMEEN, inda nake naɗar karatun littattafan Hausa da murya, ina ɗorawa. Yanzu haka akwai wani littafi da nake kan karantawa mai suna ƘAUNARMU.


Idan na ga labarin ya ba ni sha'awa, kuma na lura zai ja hankali, sai na nemi marubuciyar littafin a yanar gizo mu yi magana da ita, in ta amince sai na fara karantawa.


ADABI: Menene alaƙar aikin jarida da rubuce rubucen adabi?


HAJARU: Lallai akwai alaƙa sosai, domin suna tafiya ne kafaɗa da kafaɗa. Aikin jarida ya kasu kashi kashi, akwai ɓangaren rubutu kamar rubutun jarida ko mujalla ta takarda, da kuma irin taku ta yanar gizo, akwai kuma ɓangaren ɗaukar murya da hoto mai motsi kamar wanda ake yi a gidajen rediyo da talabijin. To, idan aka haɗa jarida da rubutu ka ga ana tafiya ne kafaɗa da kafaɗa, kuma kowanne da irin hikimarsa ta hanyar isar da sako cikin sauƙi. Wannan karantawa za a yi, wannan kuma saurare ko kallo za a yi.


ADABI: Wacce karin maganar Hausa ce ta ke da tasiri a harkokin ki na rayuwa?

Download ADABI Magazine app now

HAJARU: Alkalami ya fi takobi kaifi, sai Duniya Makaranta, da kuma 

Ba Maraya Sai Raggo!


ADABI: Madalla, mun gode


HAJARU: Ni ce da godiya. Allah ya ƙara ɗaukaka Mujallar ADABI!!!

Reactions
Close Menu