'Ina rubutu ne don gyaran tarbiyya' in ji Summie B.

 Daga Abba Abubakar Yakubu

Sunan Sumayya Babayo Abdullahi ba ɓoyayye ba ne musamman a tsakanin matasan marubuta mata masu tasowa, waɗanda ke rubuce rubuce ta yanar gizo wato online writers a turance. Kamar yadda za ku karanta a tattaunawar ta da ABBA ABUBAKAR YAKUBU, marubuciyar wacce ke nazarin aikin likitan dabbobi a babbar Cibiyar Kula da Lafiyar Dabbobi ta Ƙasa da ke Vom kusa da Jos, tana daga cikin marubutan da rubutun su ya samu yin fice a Gasar Hikayata ta marubuta mata da tashar BBC Hausa ta shirya a shekarar 2020, ta kuma rubuta ƙananan labarai masu ɗauke da darussa na jan hankali, da ta shiga gasar marubuta daban daban da su. Ga waɗanda ba su san wacece Summie B ba, kamar yadda aka fi sanin to, yadda tattaunawar ta kasance!ADABI: Ina son ki fara gabatar mana da kan ki?Hoton Sumayya Babayo Abdullahi (Summie B.)


SUMMIE B: Sunana Sumaiyya Babayo Abdullahi wacce aka fi sani da Summie B. An haife ni a garin Ɓukur da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu, a Jihar Filato, Nijeriya. Na yi karatuna na firamare a Islamiyya Primary School Bukuru, daga shekarar 2000 zuwa 2006, inda na samu nasarar tsallakawa zuwa sakandire ta Tanbihis Sunnah High School duk dai a nan garin Ɓukur daga shekarar 2006 zuwa 2012 na kammala diploma ta a ɓangaren ilimin sarrafa kwamfiyuta, wato computer science a shekarar ta 2012, na kuma sake yin wata Diploma a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Filato, wato Plateau State Polytechnic a shekarar 2015


Yanzu haka ina karatu a Kwalejin Nazarin Lafiyar Dabbobi ta Ƙasa da ke Vom, a nan Jihar Filato. Kuma ina da aure da ɗana Muhammad (Mujeed).


ADABI: Yaya aka yi ki ka samu laƙabi na Summie B?


SUMMIE B: Laƙabin Summie B, na samo shi ne a lokacin da nake aji ɗaya a makarantar sakandire, inda muke buga wasan ƙwallon ƙafa, a lokacin na samo inkiyar Summie, Summie Baby, Aunty Summie. Wannan laƙabin ya game gida da waje har yanzu da nake wannan maganar to, bayan na yi aure har na haihu idan aka kirani da Sumiee Baby nakan ji shi wani bambarakwai. Cikakken sunan dama Sumaiyya Babayo ne, don haka na mai da wancan B ɗin baby cikin wannan B ɗin Babayo. Nake amsa Sumiee B, a duniyar rubutu.


ADABI: Ko za ki bayyana mana yadda aka yi ki ka fara rubuce rubuce?


SUMMIE B: Tun lokacin da na taso na tarar da yayata mai sha'awar karance-karancen littattafan Hausa ne, nima daga wajen ta na fara samun sha'awar karatu, a lokacin ban ma iya karatun Hausa ba to, sannu a hankali dai har na koya, lokacin da nima na duƙufa karance-karance sai kuma na tsunduma cikin yin rubutu tun a waccen lokacin.


ADABI: Kawo yanzu littattafai nawa ki ka rubuta, kuma an buga su ne ko na online kawai ki ke yi?


SUMMIE B: E, zuwa yanzu ina da littattafai guda biyu, wanda na sake su online, ban buga su ba.Littafin AMINTA shi ne littafina na farko wanda ya kasance bakandamiya ta. Haƙiƙa ya samu karɓuwa fiye da tunanina. Na samu saƙonni, kiraye-kirayen waya daga mutane daban-daban daga nan gida Nijeriya har ƙasashen waje, inda ta ko'ina nake samun addu'oi, fatan alheri da sauran su. Haƙiƙa hakan ya ƙara bani ƙarfin gwiwa inda na sake baje basira da fikirata har zuwa lokacin da na kammala littafin na fara MIJIN BAHAUSHIYA.


ADABI: Mai ya bambanta rubutun ki da na sauran marubuta?


SUMMIE B: Wannan tambayar ina ga masu karatun littattafai na ne za su amsa ta. Amma bisa la'akari da zantuka da suke fitowa daga bakunan su, salon rubutu na yana riƙe zuciyar mai karatu, tare da tafiya daidai da zamani da abubuwan da suke faruwa a cikin al'umma wanda sannu a hankali kuma cikin hikima zan kawo mafita. Akasari na fi mayar da hankali ne wajen duba wata matsala ta rayuwa, kamar abin da ya shafi tarbiyya da zamantakewa, musamman tsakanin ma'aurata, da matasa. 


ADABI: Wanne ƙalubale marubutan Hausa musamman na online ke fuskanta?


SUMMIE B: Ƙalubalen bai wuce a ce ka yi rubutu ka sake shi, ba a karanta ba ko an karanta ba a ƙarfafa maka gwiwa ba daga gurin su masu karatu, wannan shine babban ƙalubalen da ke addabar mafi akasarin marubutan online.


ADABI: Wacce hanya ki ke ganin za a kawo sauyi a harkar rubutun Adabi a ƙasar nan?


SUMMIE B: A tawa fahimtar, kafin adabi ya samu sauyi a ƙasar nan dole sai an kawo hukumar tace littattafan online kamar yadda ake da hukumar tace littattafai da finafinai, rashin wannan hukumar a online ya sa ake samun taɓarɓarewar abubuwa da dama, daga su kansu marubutan da masu karatun. Abin takaici ne yadda rubuce rubucen batsa suke yawa a online, kuma an kasa hanawa, ko ɗaukar mataki mai tsauri a kai don a hana yaɗuwar su. Idan akwai wannan hukumar ita kaɗai za ta zaburar ta kuma dakatar da duk wani marubuci don tabbatar da ya tsarkake alƙalaminsa tare da yin rubutu bisa koyarwar addini da al'adar Malam Bahaushe. Bugu da ƙari a haɗa ƙarfi da ƙarfe a kafa wata ƙungiya da duk marubuta za su haɗu a kawo ƙarshen marubutan batsa, kuma a riƙa wayar wa da marubuta kai, da koyar da su dabarun rubutu lokaci zuwa lokaci.


ADABI: Wanne irin cigaba za ki bugi ƙirjin kin samu a harkar rubutu, tun da ki ka fara?


Za ka iya sauƙe manhajar ADABI Magazine app ta nan

SUMMIE B: Alhamdulillahi! Na samu cigaba da dama wanda, cikin yardar Allah dalilin rubutu na canzawa wasu tunani, ɗabi'u, halayya daga munana zuwa kyawawa. Haka zalika dalilin rubutu na zaburar da iyaye mussaman mata kan tarbiyyar yaransu. Ko a nan na tsaya ina ga ɗan koli ya ci riba.


 Aƙwai haɗuwa da manya manyan marubutan littattafai, marubutan fim, daraktoci da masu shirya finafinai da sauran su, waɗanda nake jin sunan su sai ga shi rubutu ya haɗa mu, mun kuma yi mu'amala cikin girmamawa da mutuntawa duk ta dalilin rubutu.


Bugu da ƙari, shekaru da ba su wuce biyu ba dana fara rubutu na shiga Gasar Hikayata ta mata na BBC a karon farko, a shekarar da ta gabata 2020 inda sama da marubuta 400 suka shiga daga kowanne sashi na duniya. Na samu dama da zarafin shiga cikin fitattun marubuta 12, wanda labarin su ya yi fice. Haƙiƙa na ji daɗi matuƙa, ina kuma bugun ƙirji da hakan.


ADABI: Wacce shawara za ki bai wa matasa marubuta yadda za su inganta rubuce rubucen su?


SUMMIE B: Shawara ta ga matasa marubuta shi ne, yana da kyau su fara sanin ƙa'idojin rubutu, tare kuma da jajircewa wurin tabbatar da sun yi amfani da ingantacciyar Hausa, da rubutu mai tsari, wanda zai faɗakar, ilimintar da kuma nishaɗantar da al'umma a lokaci guda. Hakan ba zai yiwu ba dole sai ka kasance mai yawan karatu, tuntuɓar masana da kuma ɗaukar gyara a duk lokacin da aka yi maka.


ADABI: A ganin ki, tsakanin marubutan zube da marubutan wasan kwaikwayo na fim, waɗanne ne saƙon su ya fi saurin isa ga jama'a?


SUMMIE B: Dukkanin su Hassana da Hussaina ne, abin da ya yi Hassana shi ne ya yi Hussaina, don haka a ganina babu wani bambanci tsakanin su. Amma idan aka yi la'akari da abin da ya ke faruwa a cikin al'umma, haƙiƙa marubutan wasan kwaikwayo suna taka muhimmiyar rawa wajen isar da saƙo, saboda yadda hoto ke yin tasiri a ƙwaƙwalwar ɗan Adam.


ADABI: Menene babban burin ki a rayuwa a matsayin ki na marubuciya?


SUMMIE B: Babban burina a rayuwata a harkar rubutu shi ne na wuce yadda nake, na kuma samu dukkanin alkhairai da albarka da ke cikinta.


ADABI: Wacce karin maganar Hausa ce ta ke da tasiri a harkokin ki na rayuwa?


SUMMIE B: Wanda bai ji bari ba, zai ji hoho!


ADABI: Malama Sumaiyya, muna godiya da samun lokacin ki. 


SUMMIE B: Ni ce da godiya. Allah ya ƙara daukaka Mujallar ADABI.

Reactions
Close Menu