Karanta 'Duk Bugun Numfashi': Gajeren Labari

'Duk Bugun Numfashi' 1k


____________________


JIGO: SOYAYYA MAI ZAFI DAGA KARSHE ARABU

______________________

Na


SAFNAH ALIYU JAWABI

_______________________________________

*

A firgice ta farka banda salati babu abinda take, gabaki ɗaya zufa ya gama jiƙa mata fuska, sauke ajiyar zuciya tayi ta janyo wayar ta dake kasan pilon da take kwance, kiran sa take babu ƙaƙƙautawa can aka ɗaga cikin Muryar bacci yace"Assalamu alaikum"

"Wa'alaikassalam kana lafiya?"

"Lafiya Kalau ke zanyi wa wannan tambayar  kinsan ƙarfe nawa kuwa yanzu?"

"Ni ban damu ba YAZID mafarki nayi mai tsoratarwa wacce sai nayi addu'ar ganin rana mutuwa ta da dai nayi arba da wannan baƙar rana"


"Amma dai kinsan cewa mafarki ba gaskiya bane ko? Yanzu dai faɗa min mafarkin da ki ka yi"


"Hmmm mafarki nayi wai ka zo har ƙofar gidan mu ka ce dani baka so na kuma baka fatan sake gani na cikin rayuwar ka"

"Kai gaskiya baki kyauta min ba"

"Meneyi maka kuma?"

"Ki duba agogon ɗakin ki da kyau ki duba karfe nawa ne yanzu"

"Karfi biyu"


"Shine kika ɗaga min hankali?"


"Au kai ta kanka ma kake kenan?"

"Sai yaushe zaki fahimci idan nace ke ina  nufin ni, idan kuma nace ni ina nufin ke? Gaskiya ki daina ɗaga hankalin ki akan irin wa'annan abubuwan dan kuwa babu wannan ranar cikin rana kun rayuwar mu, ke ce ma'adanar sirri na, kece lafiya ta,kece samuwar duk wata natsuwa da farin cikin dake gudana cikin rayuwa ta, ko murmushi nayi ki sani sanadin ki ne, haka idan kuma nayi bakin ciki sanadin ki ne,har yaushe zanyi wasa da lafiya ta kuma har na furta kalmar rabuwa a tsakanin mu, ki daina ma kawo wannan a ranki dan Allah kinji tawan?"


"Hmmm na yarda da batun ka amma duk da haka wannan mafarkin ba karamar tsoratar da ni yayi ba, ka sa ni kaine nake wa tanadin kai na, da kai ne kaɗai zan iya rayuwa, kai ɗin tamkar ruwa da jini dake gudana a jijiyar jiki na ne,dan haka rayuwa babu kai abune mai  mattukar wahalar gaske, dan Allah ka kula min da kan ka kaji Nawan?"


"In sha Allah zaki same ni mai rike miki alkawari fatan kema haka?"

"Baka da matsala da hakan kai kanka shaida ne akan haka"


"Shikenan ki kwanta ki bacci yanzu kin ji?"


"In sha Allah"


"Yawwa ki mafarki na amma ba irin wanda ki kai ɗazu ba"


"In sha Allah"


Da haka suka sauke waya,gyara kwanciya tayi tana cewa, Kashhh na mance ban tambaye shi ƙarfe nawa zai fito daka gida ba.


Shi kuwa murmushi yayi yace"Bana fatan zuwan wannan ranar cikin rayuwar mu dan kuwa rayuwa babu ke ina da tabbacin babu wani armashi a cikin ta ina mattukar kaunar ki Safnah ta.


Koda gari ya waye cikin sauri take harhaɗa kayan wanke wanken dake tare a bakin rijiyar gidan su, fitowar Umma yasa tayi saurin fara wanke wanken tana yi tana murmushi har ta gama babu abinda take tunowa sai wayar su ta jiya, wanka tayi ta sanya riga da zani, sosai kayan suka ƙarbi jikin ta, sallama tayi ɗakin Umma tana cewa"Umma na zan tafi ai mana addu'a"


"Addu'a ai kullum cikin ta kuke Yar autata sai kin dawo Allah ya tsare gaban ki da bayan ki a kula da karatu,banda shashanci"

"In sha Allah Umma na sai na dawo"

"A dawo lafiya"


Tana fita wayar ta ta fara ruri, murmushi tayi dan kuwa ko bata duba ba tasan cewa shine dan kuwa ringing ɗin sa daban ne awayar.


Ɗauka tayi ta ɗaura a kunnan ta, shiru duk sukayi na ɗan lokaci sannan yace


"Wai  menene yake faruwa ne bana ganin haske, shin har yanzu gari bai waye ba? meyasa bana iya jiyo sautin komai ko dai kurumcewa nayi ne? Meyasa nake jin kamar babu kowa a duniya sai ni kaɗai? ko dai ɗimaucewa nayi ne? Kina ina fitilar dake yayi min duhu, kina ina ne jida gani na? Kina ina mahaɗin rayuwa ta?"
"Gani nan a kusa da kai Muradin Raina,shin baka jin sahun taku na a kurkusa da kai ne? Shin baka jin yanda bugun zuciya ta ke kara tsananta saboda ina gab da isowa gurin ka? Kwantar da hankalin ka gani nan dab da kai"

"Da zaki taimaka da kin rugu da gudu dan kuwa daf nake da faɗi ƙasa warwas"


"Mintina biyu kawai zaka bani kaji Nawan?"

"Shikenan ki hanzarta"


"In sha Allah"


Cikin mintina goma sha biyar ta isa makarantar, abakin kofar makarantar yake zaune ya haɗa kai da guiwa, saukowar ta daga adaidaita yasa yayi wani irin ajiyar zuciya, cikin sauri ya isa gare ta kamar yanda itama tsabar sauri har bari wa mai adaidaita canjin tayi ta iso gare shi.


Kallon juna suke cikin ido, gabaki ɗaya banda murmushi babu abinda suke sakarwa juna, tsawon minti biyar suna a haka, Sallamar da Lubna tayi yasa suka sauke idanuwan su cikin sauri ba dan wai sun gaji ba.


"A min aikin gafara na katse muku zancan zuci"

"Tabbas akwai hukunci mai girman gaske da zanyi miki tunda kika ƙatse mana zance"

"Au ni Lubna ina ganin masifa wai yanzu ba zaki bari yayi magana ba sai ke rasa kunya?"

"Au wai hakan ma rashin kunya ce?"

"Sosai kuwa"

"Tab"


"Kinga Lubna babu wani laifi da kika yi dama can neman hanyar gudu take kawai borin kunya take miki"


"Dama nasan haka zaka ce ai idan ba tsoro ba a sake"


"Ni dai dan Allah ki zo mu tafi wallahi har malam ya shigo kuma kin san yana da zafi sosai"

"Zafin da nake ji yanzu da zamu rabu dashi yafi zafin faɗar da Malam zai min Lubna"


"Na sani amma dan Allah mu tafi dan Allah"


"Shikenan ku tafi nima ina da lecture zan tafi karna makara karki mance da alƙawarin mu dan Allah Tawan"

"In sha Allah"

"Ina mattukar kaunar ki"

"Nima haka Allah ya bada sa'a"


"Ameen ameen  kina fitowa ki jira ni a inda muke zama"


"Dan Allah Safnah mu tafi kinji lokaci yana tafiya"


"Muddun ba lokacin sallah  ba babu shakka zan iya asarar ta saboda Yazid"


Reactions
Close Menu