Kukan Kurciya (2): Yadda Faranta Ran Wani Zai Faranta Naka

 Daga Abba Abubakar Yakubu


Ko ka taba tunanin abin da ya sa mutane ke tsargar mutumin da ya cika nuna son zuciya da son kai? Mai ya sa kyauta da alheri suke daga cikin halaye abin yabawa? Mutum mai sadaukarwa da fifita bukatun wasu a kan nasa, jarumi ne a idon mutane da dama.


Yaya ka ke ji idan ka yi wani abu komai kankantarsa da ya faranta ran wani, ko ya share masa hawaye, ko kuma ya yi maganin wasu daga cikin matsalolinsa? 


Addinin Musulunci ya koyar da mu muhimmancin kyautatawa, yin sadaka da bayar da Zakka ga mabukata da raunana yana da dimbin lada mai yawa, saboda yadda hakan ke tasiri wajen canza rayuwar wasu, daga kunci zuwa sauki, daga farin ciki zuwa bakin ciki.


Wasun mu kullum bukatunsu ba sa wuce yadda za su fifita kansu ko tauye hakkin wasu, ba sa tunanin halin da wanda suka zalunta zai shiga.


An rawaito wani hadisi daga ma'aikin Allah mai tsira da aminci yana cewa, wanda ya tausayawa na kasa da shi, ubangiji wanda ke sama da shi zai tausaya masa.


Sau da dama mukan zargi wasu da nuna halayen zarmewa da son zuciya, amma muna manta cewa mu ma muna nuna irin haka, musamman ga na kasa da mu ko wanda muke ganin mun fi karfi ko babu yadda zai yi da mu. In dai mu za mu amfana, miyar gidan mu ta yi ja, mu biya bukatun iyalin mu, ba mu damu da halin da wancan zai shiga ba.


Yana daga cikin mafi kyawun dabi'u mutum ya zama mai kwadayin faranta zuciyar wani, taimaka masa, ko yaye masa wata damuwa da yake fuskanta. Ba lallai sai da kudi ba, don wani ba su ne damuwarsa ba, lokacin ka kawai yake bukata domin ka saurari damuwar sa ka bashi shawarwarin da suka kamata. Wani so yake yi ka wuce masa gaba ka jibanci lamarinsa. Wani kuwa so yake ya samu lokaci da kai ku zauna tare don ka debe masa kewa.


Misali, babban burin 'ya'ya shi ne su rayu a gaban iyayensu, su samu kyakkyawar kulawa da kauna. A wajen mace ta samu miji mai tausayawa, fara'a da sakin fuska, wanda zai bata lokacinsa don ganin farin cikinta, shi take kwadayin samu. A wajen dan kasuwa ya kasa kaya bisa farashi, masu saye su saya ya samu riba, shi ne burinsa.


Mutanen da ke samun kulawa da farin ciki daga abokan zaman su ko abokan huldarsu, sun fi nuna girmamawa da biyayya, kuma suna kasancewa masu nuna kishi don kare abin da suke samun farin cikinsu daga gare shi.


Ma'aikin Allah Annabi Muhammad, mai tsira da aminci, ya fada a wani hadisi cewa, imanin dayanku ba zai cika ba sai ya so wa dan uwansa abin da yake so wa kansa.


Haka kuma a wani hadisin an rawaito cewa, duk wanda ya yi imani da Allah da ranar karshe ya girmama makwafcinsa, duk wanda ya yi imani da Allah da ranar karshe ya girmama bakonsa.


Kyautatawa makwafci da bako, 'yan uwa da abokan arziki, halayya ce mai kyau, wacce ke nuna karfin imanin mutum, tausayinsa, da tarbiyyarsa.


Mu kasance masu nuna halayen kwarai, don faranta ran wadanda muke tare da su. Sai ubangiji ya sanya kaunar mu a zukatansu, kuma su zama masu biyayya a gare mu, ba tare da tunanin cutarwa ba.


Allah shi ne masani!

Reactions
Close Menu