Kukan Kurciya (3): Girman Kai Rawanin Tsiya

Tare da Abba Abubakar Yakubu 


Wannan karin magana tana nuni ne da illar mutum ya kasance mai nuna girman kai, raina mutane da nuna fifikon sa da sauran mutane. Nuna halayyar ni na fi ƙarfin a yi min kaza, ko na wuce a yi min abu kaza.


Girman kai na daga cikin munanan halayen da ake ƙyama tare da nisantar mutane masu nuna wannan halayya. Mai nuna halin girman kai bai cika shiri da mutane ba, kuma yana kasancewa mai yawan rikici da mutane, saboda ba ya ba da uzuri ga kuskuren da aka yi masa.


Masu girman kai suna nisanta kansu da arziƙi da soyayyar mutane, kuma suna tsallake damarmaki da yawa da gangan ko cikin rashin sani.


Girman kai na daga cikin halayen 'yan wuta, kamar yadda wani hadisi ya kawo. Don haka ba hali ne da aka san mutanen kirki ko Musulmin ƙwarai da shi ba


Ya kamata mu riƙa fahimtar cewa, duk abin da addini ya koyar game da halayen ƙwarai yana da nasaba wajen samun tsirar mutum duniyar sa da lahirarsa.


Ma'aikin Allah, Annabi Muhammad (SAW) mutum ne mai matukar sauƙin kai da rashin nuna fifikon sa a cikin mutane. Yana mu'amala ta ƙwarai da makusantansa da na nesa da shi, yana nuna girmamawa da martaba mutane, ba tare da ware wannan ɗa ne ko bawa ba, faƙiri ne ko attajiri ba ne.


Waɗannan na daga cikin halayen da suka kara sanya ƙaunarsa a zukatan jama'a Musulmai da waɗanda ba Musulmi ba. 


Akwai wasu mutane da ba sa sassautawa na ƙasa da su, kuma hatta waɗanda suka girme musu ko suke gaba da su ba sa mutunta su.


Idan har kana haka domin a zatonka hakan ne zai sa a riƙa ganin girmanka, shakkar yi maka raini ko kusantarka to, a maimakon ka samu yadda ka ke so daga wajen mutane sai ma ka samu akasin haka. Mutane za su tsane ka, a daina kusantar ka da duk wani abin alheri ko girmamawa.


Yana daga munanan halayen da ake tir da su, a kowacce al'umma da kowanne addini. Har ma Musulunci yana nisanta kansa da mutumin da mutane ke shakkar sa don munin halinsa.


Duk mai son ya yi mutunci a idon mutane to, ya mutunta kowa, shi ma kuma ya tsare mutuncinsa. Sannan Wanda yake son a girmama shi ya girmamawa duk wanda hulɗa da zaman tare suka haɗa su. Ma'aikin Allah (SAW) yana cewa, ku girmama furfura ko da ta kafiri ce. Ma'ana, mutum ko ba Musulmi ba ne a girmama shi, domin wasu na ganin sa da martaba. Shi ya sa ba a son a wulaƙanta shugabanni da raina magabata.


Duk wanda Allah ya sa shi ne gaba da kai, a wajen aiki ko a makaranta to, ka ba shi girmansa, ko da kuwa ka girme shi ko ma ɗanka ne. A dalilin haka shi ma sai ya ba ka naka girman, ba tare da wani raini ko ƙasƙanci ba.


Allah ya karrama dan Adam kuma ya faɗa a Alkur'ani mai tsarki, an rawaito daga hadisai yadda kyakkyawar mu'amala take sanya ƙauna da zaman lafiya.


Mu guji nuna halayen da za su sa jama'a murna da jin labarin mutuwar mu, ko kuma idan wani abu ya samu mutum a riƙa cewa ai gara da haka ta faru da shi, don mugun halinsa na rashin martaba mutane da wulaƙanta raunana. 


Tarihi ya kawo labaran manyan ƙasashe da manyan masu mulki ko dukiya irin su sarkin Ruma da Fir'auna da Hamana da wasun su da dama, waɗanda ke ganin sun fi kowa, kuma kowa a ƙasan su yake har ubangiji mahaliccin duniya (wa'iyazubillah)! Amma a ƙarshe yaya suka kasance? Sun mutu a wulaƙance kuma har duniya ta tashi za a ci gaba da ambatar munanan halayen su ana la'antar su. 


Mu ne kaɗai za su samar wa kawunan mu shaida tagari da sunan ƙwarai, wanda da zarar an ambace mu a wani waje, a raye ko a mace za a yi mana addu'ar alheri. Allah ya sa mu fi ƙarfin zukatan mu!

Reactions
Close Menu