Mujallar ADABI za ta ɗau nauyin buga labaran marubutan yanar gizo guda 500 a matsayin littafi

 


Kamfanin dillancin labarai na Mujallar ADABI zai ɗauki nauyin bayar da horo na musamman kan koyar da dabarun rubutu gami da darusa a kan ƙa'idojin rubutun Hausa ta hanyar yin haɗin gwiwa da tsofin marubuta da kuma shehunnan adabi. Wannan wani gagarumin yunƙuri ne da kamfanin yayi don tallafawa marubutan zamani dake amfani da kafar sadarwar zamani ta intanet wajen ganin sun samu wadataccen ilimi kan dokokin harshen da suke amfani da shi wajen rubutu inda hakan zai taimaka musu wajen bunƙasar ayyukan su tare da ƙara musu yawan damammaki na yiwuwar lashe ƙanana da ma manyan gasannin labarai da wasu gidauniyoyin, kamfanoni da kuma hukumomi ke sa wa lokaci bayan lokaci. 

Hakanan wannan matakin tsani ne da marubutan za su samu shaidar tabbatar da ƙwarewar su daga Mujallar ADABI wadda ta kasance babbar kafar sadarwa ta labaran Adabi daga dukkan kusurwoyin duniya wadda ke ɓulla zuwa ƙasa da ƙasa. Bugu da ƙari, burikan marubutan da matsalar rashin kuɗi ya hana su wallafa littatafan su zai cika tunda Mujallar ADABI ta samar da tsarin da zai share musu wannan hawayen.


Yadda Aikin Samar Da Littafin Zai Kasance:


1. Mujallar ADABI za ta koyar da marubutan da suka samu damar shiga ajin darussan akan lokaci, darusa akan ƙa'idojin rubutun Hausa wanda aka shirya shi mataki-mataki kuma bi da bi cikin matuƙar sauƙi. 


2. Bayan kowane ƙarshen makon darasi akwai aikin jinga da malaman dake karantarwa zasu bayar ga marubutan wanda zasu amsa. 


3. A kowane ƙarshen makonni biyu akwai bitar ayyukan da aka yi tare da ƙaramar jarrabawa wadda a nan za a na bayyana sakamakon ɗalibai mafiya hazaƙa tun daga kan na ɗaya har zuwa na biyar. 


4. A ƙarshe kowane wata ɗaya, za a buƙaci marubutan dake ɗaukar darasi da su zaɓi jigon da suke da buƙatar yin rubutu tare da rubuta labari ta hanyar kiyaye abubuwan da suka koya a aji wato ta hanyar bin dokoki da ƙa'idojin rubutun da aka koyar da su. 


5. Malaman da suka koyar da marubutan za su bi labaran tare da yi musu maki. Labaran da marubutan suka kiyaye abinda suka koya a aji tare kuma da ma'anar jigon da suka ɗauka wajen rubutun su ne zasu fi samun yawan maki.


6. Labarin da ya samu maki 50% zuwa sama su ne labaran da malaman zasu miƙawa Mujallar ADABI a kowane ƙarshen wata tare da bayanan marubutan da suka rubuta su.


7. Marubutan da aka soke labaran su aƙalla sau biyu zuwa uku, za a mayar da su ajin bada kulawa ta musamman inda za a koyar da su ta hanyar saƙonnin bidiyo da kuma murya don tabbatar da sun koyi darusan. Anan za a sake ba su wata damar na yi nasu labaran.


8. Manufar ita ce koyar da rubutu da cikawa marubuta masu son ganin sun wallafa littafi burin su na ganin mafarkin su ya cika. Don haka babu korar ɗalibin dake da muradin koya sai dai wanda ya kori kansa.


9. Wannan salon zai cigaba da tafiya har zuwa ranar da Mujallar ADABI za ta gudanar da bikin cikar ta shekaru biyar da kafuwa. A wannan lokacin za a tuntuɓi dukkan marubuta tare da sanar da su tsarin yadda bikin murnar zai kasance tare da na ƙaddamar da littattafan na su a lokaci guda inda bayan littattafan kuma duk za a ba su shaidar dake nuna ƙwarewar su wajen iya rubutu bisa ƙa'idojin rubutun Hausa.


10. Za a gudanar da azuzuwan ne da kuma jarrabawar bitocin a zauren AJI KARATU dake manhajar Mujallar ADABI. Don haka matakin farko shi ne sauƙe manhajar mu ta mujallar ADABI tare da yin rajista don zama a shirye.


Duk mai tambaya zai iya yi mana a Zauren Mujallar ADABI na WhatsApp. Ba zamu samu damar amsa tambaya a wajen zauren ba saboda gudun maimata tambaya iri ɗaya.Za a iya shiga zauren ta wannan link ɗin amma ba a kawo wani batu da ba shi da alaƙa da ADABI.


https://chat.whatsapp.com/I59YHzjeHTFAm8eWTF3ZhO

Reactions
Close Menu