Wani Uba...!: Gajeren Labari


WANI UBA...!


NA

HASSANA ƊAN LARABAWA


Kukan da Asiya ta ji shi ne ya sa ta fito daga cikin ɗakin ta da sauri zuwa tsakar gida, yarinyar da bata fi shekaru goma sha biyu ba ta iske a tsaye sai sharar hawaye take. A hankali ta ƙarasa kusa da yarinyar ta dafa kafaɗarta ta ce.

"Murja lafiya kike kuka? Me ya faru?"

Hawaye ya sake ɓallewa Murja,cikin shessheƙar kuka tayi magana.

"Yusra ce take wasan banza da maza a waje, wai don na ce mata ta daina wasa da maza saboda me aikata hakan ta zama ballagaza,shine ta gayawa Buhari ya kama zagina yana dunguri na,kuma har da fito da wuƙa yana nuna ni da ita ina kaucewa,kinga ma har ya yanke ni a hannu na" Murja ta ƙarashe maganar tana sake rushewa da kuka.

Tsananin ɓacin rai da damuwa ne suka bayyana a fuskar Asiya, musamman da ta kalli hannun Murja ta ga har yana fitar da jini, ɗaki kawai ta koma ta sako hijabi tayi hanyar ƙofar gida tana faɗin.

"Murja ki jira ni ina zuwa."

Tana leƙawa wajen ta hango yaranta mata guda uku sai wasan banza suke suna wasan langa da maza, ƙwalla ta zubo mata akan fuskarta saboda tsabar baƙin cikin halin da y'ay'an cikinta suka kasance,yanzu kuma bata da damar yi musu magana sai cibi ya zama ƙari.A gaban su mahaifinsu zai ci mata mutunci ya zageta,idan ta kai gargara ma yana iya kifa mata mari duk don ya tozarta ta,share hawayen ta tayi ta kalli gefen da Buhari ya ke,wuƙa ce a hannun sa yana ta ferayar rake,shekarunsa na haihuwa guda goma sha ɗaya ne kacal.
       
       Sai da ta ambaci sunan sa sau biyar sannan ya ɗago ya kalleta, yana ɓata rai yana wani cije baki,ta ɗauki kusan minti bakwai a tsaye tana jiransa,sai da ya gama feraye raken hannunsa sannan ya miƙe ya nufo in da take tsaye,juyawa tayi ta shige cikin gidan shi kuma ya bita a baya har zuwa ciki.

Suna shiga ya ga Murja a tsaye tana kuka,ya dalla mata harara har da sakin tsaki da faɗin "Banza !munafuka!" Wannan ya fusata Asiya ta waiwayo ta fidda hannu ta tsinka masa mari tana hucin ɓacin rai,sannan ta balbaleshi da faɗa akan abin da ya aikatawa Murja.

Buhari ya dafe kunci saboda zafin marin,har Asiya ta gama faɗanta,buɗar bakinsa sai cewa yayi.
"To ni akan me zaki mareni?Allah ya isa ban yafe miki ba! "

"Ni kake wa Allah ya isa Buhari?ni mahaifiyarka da na tsuguna na haifeka?" Asiya ta ambata tana dafe ƙirjinta cikin zare idanu.

"Ya yi miki Allah ya isan,idan akwai abin da yafi Allah ya isa ma zan so yayi miki,muguwa azzaluma mai baƙin hali,ki rasa y'ay'an da zaki dinga duka sai y'ay'an cikin ki,ina nan ina addu'ar Allah ya kawo ranar da zaki ɗaga hannu ki daki yaran nan su fidda hannu su rama Asiya." Wannan kalamin ya fito daga bakin mahaifinsu Buhari ne.Wanda ya shigo gidan a lokacin ya riski abin da ke faruwa.
Hawaye ne mai zafi ya tsinkewa Asiya,zuciyarta kamar ta faso ƙirjinta ta fito saboda azabar raɗaɗin da take mata,amma duk da hakan daurewa tayi ta dubi mijin nata cikin rawar murya ta ce.

"Baban Yusra a kullum ina ƙara tunasar da kai cewar waɗannan abubuwan da kake yi basu kamata ba,burinka a kullum ka hurewa yaran nan kunne akan ƙin bin umarni na da yi min biyayya,ni mahaifiyarsu ce,ni na tsuguna na haife su,amma ka rabani da su kana nuna musu aibuna,duk ka sa sun raina ni basa ganin girmana ba sa jin magana ta,duk wanda ya dubi yaranmu zai ga babu wata tarbiyya a tare da su,babu ilimin boko balle na arabiyya da ya zame musu wajibi,baka damu suje makaranta ba,baka damu suyi sallah ba,baka damu da koya musu yadda za su bi Allah(S W A) ba. Idan nayi yunƙurin saita su a hanya ka dankwafar da ni,wannan wace irin rayuwa ce? Haka kake so y'ay'anmu su tashi tamkar wasu dabbobi? Ka duba kamar Buhari har ya san ya ɗauki wuƙa ya yanki yarinyar mutane da sunan faɗa,ka dubi yaranmu mata a waje suna wasannin banza da maza,shikenan mu haka rayuwar mu zata kasance kenan Baban Yusra?
Da ni da yaran gabaɗaya fa kiwo ne a hannunka,kuma wallahi kar ka manta akwai ranar da Allah zai tambayeka akan kiwon da ya baka,duk wannan abin da ka ke musu ba soyayya ba ce,illa lalata musu rayuwa da ka ke yi." Duk waɗannan maganganun Asiya tana yin su ne cikin kuka da ƙunar zuciya.

A maimakon Lawal (Baban Yusra) yayi nadama, sai ma ya ƙara balbale Asiya da masifa yana kumfar baki, har da fitar da hannu ya dalla mata gigitaccen mari ,a yunƙurinsa na ramawa Buhari marin da tayi masa.A gaban yaron kuma ya dinga zaginta yana ci mata mutunci,bai kuma tsaya anan ba sai da ya leƙa ya kirawo ragowar yaransu mata ya haɗa su yayi musu nuni da Asiya ya ce musu.

"Kun ga wannan matar? Duk da tana mahaifiyarku ba ƙaunarku take ba,muguwa ce azzaluma, dan haka ina umartar ku duk lokacin da ta zage ku to ku rama,idan kuwa ta dake ku kuma ku fidda hannu ku rama,idan kuma ba zaku iya ba idan na dawo ku faɗa min ni zan rama muku da kaina.Sannan ko a waje kar ku dinga ragawa kowa,duk wanda yayi muku to kuma kuyi masa,kar ku damu kuna da uban da zai zame muku kariya a koda yaushe y'ay'ana,ni ne gatanku."

Haka ya dinga yi musu huɗubar sharri suna ɗaukewa suna yi wa uwar su kallon banza,daga ƙarshe ma cewa yayi su tashi ya kaisu kanti su sayi dukkan abin da suke so,cikin murna suka rankaya suka fice,suka bar Asiya tsaye tana kukan baƙin cikin wannan bahaguwar rayuwa.


 SHEKARUN BAYA DA SUKA SHUƊE

Asiya ta auri Lawal ne ba da son ranta ba,sai dan babu yadda zata yi,Lawal ya kasance malamin mata,wanda mata suke kwasar jiki su kai masa damuwar su,take shi kuma zai haɗa surkullen sa ya basu a matsayin magani,ba iya nan ya tsaya ba,ana kai masa mata masu lalurar aljanu domin yi musu magani.

    Haɗuwar sa da Asiya ta samo asali ne a ranar da mahaifiyar ta ta kaita domin ayi mata maganin mutanen ɓoyen da ke damunta,cikin ikon Allah ba a ɗauki lokaci mai tsawo ba sai Asiya ta warke,suka nemi ya faɗi ladan aikinsa. A take Lawal ya ce "Ku bani Asiya na aura,wannan shine ladan aikina" .Asiya ta so bijirewa domin bai yi mata a matsayin kalar mijin da take so ta aura ba,Lawal bai yi ƙasa a gwiwa ba, wajen yi musu barazanar dawowa da Asiya aljanu jikinta fiye da na baya,muddin bata amince ya aure ta ba,nan iyayen ta suka lallaɓata ta amince ba tare da son zuciyarta ba.
Bayan aurensu Asiya na haƙuri da yadda ta samu halayen Lawal marasa kyau,saboda babu yadda zata yi da shi,ko nasiha tayi masa sai dai ya zageta,wataran ma har da duka,ko ta je gida ta faɗawa iyayen ta ba sa yarda,saboda yadda Lawal ya ɗaure musu baki,sai dai ta shaƙi baƙinciki tayi kuka ta godewa Allah.Idan tayi sallah kuma ta nemar wa mijinta shiriya wajen Allah.
  
      A haka rayuwar ta ci gaba da tafiya har Asiya ta haifi y'ay'a guda huɗu tare da Lawal,babbar ita ce Yusra,sai mai bi mata shine Buhari,sai Saudat,sai kuma ƙaramar wato Nusaiba.Dukkan su sun taso cikin sangarta da rashin tarbiyya ne,Lawal ya lalata su ta yadda basa ganin girman kowa hatta ita mahaifiyarsu da ta haife su.Idan taga wasu yaran na kiran mahaifiyarsu da (Umma ko Mama) har sha'awa take,saboda ita kai tsaye yaranta gatsal suke kiran ta da Asiya,kuma ubansu Lawal ne ya koyar da su hakan.
Allah ya gani kuma ya shaida tana iyakar ƙoƙarinta wajen ganin tarbiyyar yaran ta gyaru,amma Lawal ya hana hakan,babu wata rana da za ta fito ba a kawo mata ƙarar ɗaya daga cikin yaran ta ba,maƙota kuwa har sun gaji da zuwa faɗa mata cewar ta kula da tarbiyyar yaran ta,idan ta yiwa Lawal maganar sai dai cin mutunci ya biyo baya,da taga hakan sai ta koma kai kukan ta ga rabbil izzati akan ya kawo mata ɗauki kan rayuwarta da ta y'ay'an ta.

    Lokacin da yaran suke ƙara girma,a lokacin ne abubuwa suke ƙara cakalkalewa.Yayin da Lawal ya tsunduma cikin harkar dillancin filaye da gidaje,ya fara baya-baya da sana'ar bawa mata magani.


DAWOWA LABARI


Addu'a takobi ce ta muminin ƙwarai! kuma dalili ne babba na rabauta da alkairai da albarkatai,haka nan tana yaye baƙinciki da sharri da bala'in duniya.Haƙiƙa Allah ya yi umarni da addu'a a cikin ayoyi masu yawa,ya ce.

"و قال ربکم ادعونى أستجب لکم"

(Kuma Ubangijinka ya ce,ku roƙe ni,na amsa muku).

   Dalilin da ya sa Asiya bata taɓa gajiya da addu'a da kai kukan ta zuwa ga Allah ba kenan! ta tsananta kwaɗayin ta ga Allah Ta'ala wajen neman biyan buƙatun ta.Kuma da ya ke Allah (Sami'uddu'a'i) ne sai ya amshi roƙon ta ya shiryi y'ay'an ta mata,suka zama masu hankali da nutsuwa kamar sauran yara,duk da mahaifin su kuma bai saka su a makaranta ba ita tana zaunar da su a gida ta koya musu abin da ta sani daga cikin addini.

   Buhari ne kawai al'amuran sa ke ƙara taɓarɓarewa,lokacin da ya shiga shekara ta goma sha biyar har shaye-shaye yake yi da sace-sace,amma Lawal bai taɓa damuwa da halin da yaron yake ciki ba harkar gaban sa kawai ya ke,shi a ganin sa ai gata yake wa yaran,ya manta da karin maganar da hausawa ke yi wajen faɗin( Ka ƙi naka duniya ta so shi,ka so na ka duniya ta ƙi shi).
Ita dai Asiya duk da hakan tana godiya ga rabbil izzati da ya shirya mata y'ay'a matan,shi ma kuma Buharin ta na cigaba da nemar masa shiriya wajen Allah.Duk da tana ji a jikin ta cewar shiriyar Buhari za ta tabbata ne bayan ya zame wa Lawal izina da ishara a rayuwar duniya kafin a je lahira.

 A wata rana da babban tashin hankali ya wanzu a gidan,sun wayi gari ne an sace kuɗin da Lawal ya ajiye kimanin (Naira dubu ɗari biyu da hamsin),kuɗin cinikin wani fili da aka yi,kuɗin ma ba nasa bane ajiya aka bashi,shine aka wayi gari babu kuɗin babu alamar su.Tashin hankalin da Lawal ya shiga ba shi da misali,ya gigice ya ɗimauce ya fita daga hayyacin sa,bala'i yake wa Asiya akan ta fito masa da kuɗin sa idan ba haka ba zai iya ganin bayan ta akan wannan kuɗi,Asiya tayi kuka kamar hawayen ta zai ƙare,ta rantse masa da Allah akan ba ita ta ɗauki kuɗin ba,tunda tun zaman su tsawon shekaru ƙwandalar sa bai taɓa nema ya rasa a gidan ba,amma Lawal ya ƙi yarda,ya tubure akan shi fa sai ta fito masa da kuɗin sa a lokacin.

   Ana cikin hakan Allah ya kawo Buhari,ya sha yayi mankas da shi,ya tarar da dambarwar da ake yi,take ya buɗe baki ya cewa uban shine ya saci kuɗin,kuma sun je sun kashe a (birthday),wato bikin tunawa da zagayowar ranar haihuwar abokin sa (Tajo).Nan take hankalin Lawal ya tashi matuƙa,ya cakumi Buhari yana dukan sa da zagin sa akan ya fito masa da kuɗin sa ,Buhari ya fusata ainun da abin da Lawal yayi masa . A take ya zaro wuƙar da ke soke a ƙugun sa ya fara kaiwa Lawal sara da ita,kafin ka ce me yayi masa yanka da yawa cikin jikinsa,Lawal ya faɗi ƙasa kwance cikin jini,yayin da Asiya da sauran yaran ke ihu da kururuwar neman taimako,shi kam Buhari yana cika aiki ya yar da wuƙar ya arce ya bar unguwar.

    Haka aka kwashi Lawal aka yi asibiti da shi bai san inda kansa yake ba,har yatsun sa guda biyu sai da suka fita daga jikinsa tsabar yankan da ya sha,ya sha wahala matuƙa a asibiti kafin ya fara farfaɗowa,Asiya ce ke hidima da shi,duk ta siyar da kayan ta wajen neman kuɗin magani.Da Lawal ya fara warkewa kuka yayi kukan nadama har kamar idanuwan sa za su tsiyaye,Asiya kuwa har gajiya take da neman gafararta da ya ke yi,sai dai ta ce masa "Ka nemi gafarar Ubangiji,in dan ta ni ce na yafe maka Baban Yusra"

Babu abin da ke ɗaga hankalin Lawal idan ya tuna wai ɗan da ya nuna wa so shine ya nakasta shi,kullum fatansa Allah ya kawo ranar da Asiya za ta doki Buhari shi kuma Buharin ya rama,to yau ga fatansa ya afka kan sa,Buhari bai doki Asiya ba amma shi ya doke shi,Idan ya tuna hakan bai san lokacin da ya ke fashewa da kuka ba.

Sai da aka yi kusan wata biyu sannan aka samu labarin Buhari ashe lagos suka gudu shi da abokan shashancin sa,Asiya ta nemi a kamo shi dan a hukunta shi akan abin da yayi ,amma Lawal ya dakatar da ita yana hawaye ya ce.

"Rabu da shi Asiya,duk wasu abubuwa da Buhari yake aikatawa marasa kyau ni ne sila,ni ne mai laifin ba shi ba,na kasance WANI UBA mara alfanu ga rayuwar y'ay'an sa,addu'a ta da fatana Allah ya yafe min laifukan da na aikata a baya."

"Ameen ya rahman" Asiya ta amsa hawaye na biyo kwarmin idanuwan ta. Tana ji a ranta za ta cigaba da addu'a akan Allah ya shirya mata Buhari shi ma.ƘARSHE!
08080049548
Reactions
Close Menu