Karanta 'Ba zato!' Gajeren LabariBA ZATO!

RUBUTAWA: HASSANA ƊAN LARABAWA


BA ZATO na ji sakkowar hawaye a kan kuncina, sakamakon tuna mahaifiyata da na yi, wacce na rasa ta kimanin shekaru goma da suka shuɗe. Zubar hawayen nawa ya wanzu ne dalilin tunawa da maganar da ta yi mini lokacin da ruhinta yake gab da baƙuntar lahira.


"Ƙasa za ta rufe idanuwana ba tare da na ga auren ki ba Binta! Ashe dai wannan gyambon da ke zuciyata ba zai warke ba kafin na bar duniya, yau da nake hango tabbatuwar kushewata nan da lokaci ƙanƙani sai nake jin zuciyata ta yi rauni fiye da yadda ta ki zuciyar take da rauni a shekarun baya."


Na sauke numfashi ina kallon tulin takardun da ke gabana a kan teburi, zuciyata ta ci gaba da yi mini zafi, hawaye na sauka.


"Ban gargaɗeki akan kar ki kuma tako ƙafarki gidan nan ba Binta? Na daɗe ina jaddada miki kallon fuskar zaki ta fiye mini alheri akan kallon baƙar fuskarki. Tashi ki fice mini daga gida tun kafin na wanzar miki da wulaƙancin da ba ki taɓa ZATO ba."


Kalaman Mahaifina suka faɗo mini a rai, lokacin da ya yi mini korar kare saura awa ɗaya mahaifiyata ta bar duniya. 


Na yi ƙasa da kai; na kwantar a jikin teburin da ke gabana, ina tuna lokacin da ya fizge hannuna daga jikinta ya yi wurgi da ni. Har ta fashe da kuka tana daga kwance, kukan da ya janyo mata tari mai tsananin ƙarfi "Ki yi hak'uri Binta. Allah yana tare da ke kuma Abubakar ma yana tare da ke, kuma na tabbatar za ki cinye jarrabawarki ko babu ni a filin duniya."


Ƙwanƙwasa ƙofar da a ka yi shi ne musababbin katsewar tunanina, na kai hannu na goge hawayen da ya ɓata mini fuskata. Na yi jarumtar aro nutsuwa sannan na bayar da izinin shigowa.


Sister Rafi'a ce ta turo ƙofar ta ƙaraso gabana tana, ta risina cikin girmamawa.


"Ranki ya daɗe akwai mara lafiyar da aka kawo yanzu, kuma (Emergency) ne. Na sanar da su kin tashi daga aiki amma sun dage akan na sanar da ke ko za ki taimaka musu."


Na sauke ajiyar zuciya, na mik'e na d'auki jakata da mukullin motata na dube ta na ce,

"Taimakon ba shi ne matsalar ba Rafi'a. Makarar da zan yi wajen isa gida domin na tanadar wa Yaya Baffa abin buɗe baki shi ne abin dubawa, ko kin manta yau rana ce ta Litinin?"


Ta ce "Ban manta ba. Naci da roƙon da suke ta yi mini shi yasa na zo, don kar su ga kamar ina ƙin a taimaka musu ne." 


Na nufi ƙofar fita, sannan na waiwayo na dube ta.

"Ki ba su haƙuri. Kuma ki sanar da su muhimmin uzurin da ke gabana, wanda ba don shi ba zan iya sadaukar da lokacina wajen taimakon su."*********


"Ina fatan an dace?"

Ƙasaitaccen mutumin mai cikar haiba ya ambata bayan Rafi'a ta Ƙarasa gabansu. Ta girgiza kai ta sauke numfashi.

"Ai dama na faɗa muku. Tana da babban uzuri ne da ya saka dole ba za ta iya tsayawa ba, ga ta can tana ƙoƙarin tafiya gida ma." Ta ambata lokacin da na gifta ta gefensu na nufi harabar asibitin. 


Ya bi inda ta nuna da kallo cikin dukan zuciya, bayana kawai yake iya hange, ya juya ya kalli dattijuwar mahaifiyarsa da take ta juya kai saboda azabar ciwon kunne da ke addabar ta, ya sauke ganinsa kan budurwar ɗiyarsa da ke riƙe da hannun mahaifiyar tasa tana hawaye da jero mata sannu.

Cikin tafiyar sauri da kuzarin da yake da shi ya yi hanyar harabar asibitin, ta juya da sauri tana duban sa, ta sanya murya da ƙarfi ta ambaci sunan sa "Daddy! Ina za ka je?" Bai waiwayo ba balle ya tanka mata; illa sauri da ya ƙara domin ya cim ma inda nake tsaye ina ƙoƙarin buɗe motata. Ganin hakan sai ta saki hannun tsohuwar ta tashi da sauri ta biyo bayansa.


"Haba baiwar Allah! Wane irin rashin imani kike da shi da za ki sa katangar ƙarfe ki rufe idanuwanki daga taimakon tsohuwar da na tabbatar ta haife ki ko ma ta yi jika da ke. Jikin mahaifiyata yana da darajar da ya fi ƙarfin ƙananan likitoci irin ku su taɓa shi. Ƙaddara ce kawai ta kawo mu."


A hanzarce na juya, kalamansa na dukan zuciyata; idanuwanmu suka gauraya da juna duk da nasa suna rufe cikin tabarau mai garai-garai. Cikar surarsa bai ɓoye tsufan da ya fara bayyana a fuskarsa ba, ta hanyar farar furfura tsilli-tsilli da ke jikin baƙin gashin gemunsa.


"Lah! Daddy ga Mummy na."


Da ni da shi a tare muka kai kallonmu kan budurwar da ta yi maganar cikin shauƙi. Dukkanmu muka zaro idanuwa a lokacin da ta kwaso sauri ta afka kan ƙirjina tana faɗin "Mummyna. Ashe zan sake ganin ki?"


Sandarewa na yi a tsaye saboda jin yadda ta ƙanƙameni tamkar ta koma cikina ta ɗago daga jikina ta riƙo hannuna.


"Mummy! Kamar ba ki gane ni ba ko? Khausar ce fa." Ta ankarar da ni don ga ZATONTA ban shaida ta ba. A take sai ƙwaƙwalwata ta shiga tariyo mini farkon haɗuwata da ita.


Wata ranar Juma'a da ta kasance ana walimar bikin ƴar ƙawata Hajiya Zulaihat.; walimar da ta haɗa da iyayen amarya da ƙawayensu da amarya da ƙawayenta, kowa ka gani cikin farinciki da walwala, amma ni tawa zuciyar a matuƙar ƙuntace take. Shekaruna suna ta ja har sun kai adadin arba'in da uku. Ƙawayena sun fara aurar da ƴaƴan da suka haifa, ni kuwa ina bilinbituwa a sararin duniyar da ba a halicci wani namiji da zai so ni ba. Hankalina ya zurfafa wajen tunani a lokacin da na ji hayaniyar mutane sama da biyar a kaina. Na dawo cikin hayyacina ina bin su da kallo, idanuwana suka faɗa kan wata budurwa guda ɗaya da ta kasance cikin ƙawayen amarya, tana ta rawar jiki tana nuna ni da ɗan yatsan ta ga ragowar mutanen da ke zagaye da mu "Kun ganta ko? Nusaiba ku kalli fuskarta. Don Allah ba ta yi muku kama da hoton mahaifiyata da na taɓa nuna muku ba?"


"Tabbas sun yi matuƙar kama, kamar an tsaga kara." Wadda aka ambata da sunan Nusaiba ta faɗa cikin ƙura mini ido da mamaki kan fuskarta.

Budurwar ta ƙaraso gabana ta gurfana. "Tun ɗazu idanuwana suke ta kallonki dalilin kamannin mahaifiyata da ke zane a kan fuskarki. Ban sani ba ko idanuwana ke mini gizo, shi yasa na tattaro ƙawayena su taya ni alƙalanci."


A take na gane kamannina ne suka yi kama da kamannin mahaifiyarta. Sai na yi murmushi na riƙo hannunta "Allah sarki! Zan so na ga mahaifiyar taki kuwa, domin na ga wannan kama da kuke ta zuzutawar mun yi ni da ita."


"Ta yi mini nisa; ta rasu kimanin shekaru biyar da suka wuce." Ta amsa mini hawaye na sakko mata.


"Wayyo Allah ya jiƙanta!" Ni ma zuciyata cike da raunin tuna mahaifiyata.


"Ameen Mummyna!"


 "Ya ya sunan ki ne y'ammata?" Na tambaya ina jin daɗin ambato na da ta yi da Mummy.


 "Khadija sunana, amma Daddyna yana kira na da Khausar saboda sunan mahaifiyarsa ne."


Tattaunarmu ta katse a lokacin da ta amsa kiran Yayanta a waya; inda ya sanar da ita zuwansa domin ya ɗauketa. Na miƙa mata wayata kafin ta tafi ta sanya mini lambarta domin ɗorewar zumunci, daga nan muka yi sallama kamar ba za mu rabu ba. Ta ja zugar ƙawayenta suka wuce.


Bayan kammala walimar ne a wajen tururuwar fita, aka zare mini wayata da ke cikin jaka; ban ankara ba ma sai da na je gida ina laluben ta na ji wayam. Dalili kenan da na rasa lambar Khausar.


*********


Na sauke numfashi bayan na tuna. Kafin na yi magana ta riga ni "Mummy kin tuna ni yanzu ko?"


"Tabbas na tuna ki Khausar." Ta yi tsallen murna ta nufi mahaifinta ta jingina da jikinsa, cikin shauƙi ta ce masa,


"Daddy ka tuna labarin da na taɓa ba ka akan na ga mai kama da Mummyna? Wannan ce fa, sun yi kama ko?" 


Ya yi murmushi "Tabbas sun yi kama a sura. Sai dai bambancin halayya."


"Kamar ya ya kenan Daddy?" Ta tambaye shi cike da zaƙuwa.


Ya ce "Mummynki tana da kirki da tausayi, ita kuma wannan ban hangi hakan a tare da ita ba; 'Juma'ar da za ta yi kyau tun daga laraba ake ganeta' tana shirin guduwa kawai don ta gujewa duba lafiyar Hajiyata?"


"Ba haka ba ne Daddy 'mai ɗaki shi ya san inda ke masa yoyo' ƙila tana da uzuri ne."


Duk da maganganunsa sun wa zuciyata karan tsaye sai na ji ina da sha'awar taimakon mahaifiyarsa ko domin Khausar. Da kaina na ja hannunta muka koma ciki. Babu ɓata lokaci na sa aka kai mini dattijuwar ɗakin duba marasa lafiya na yi mata dukkan abin da ya dace. Cikin lokaci ƙanƙani sai Allah ya kawo sauƙi.

Ina kammalawa wayata ta yi ƙara, na ɗaga a sanyaye, muryar yaya Baffa ta sauka a kunnuwana bayan ya amsa sallamar da na yi "Kar ki ga shiru ban dawo ba, ƙarfen nasara ba shi da tabbas; yanzu haka ina dab da asibitin ku wajen kanikawan nan."

Na ce "Ni ma ban koma ba Yaya. An kawo mara lafiya ne na tsaya duba ta."

"Babu laifi, bari na ƙaraso sai mu wuce gida tare." Ya kashe wayarsa.


Minti ashirin tsakani yaya Baffa ya bayyana. Tun a farfajiyar suka haɗu da Daddyn Khausar, take suka gane juna saboda sun haɗa jam'iyyar siyasa, suka gaisa tare da nufar ofishina. Ba su iske ni can ba sai suka nufi ɗakin da na duba Hajiyar, suka same ni muna ta hira kamar mun saba da juna.

"Wai daman Alhaji Abubakar wannan likitar matarka ce?" Daddyn Khausar ya tambayi yaya Baffa cike da mamaki.

"Ba matata ba ce, ƙanwata ce." Ya amsa masa tare da yi wa Hajiya sannu.


Mun fito za mu tafi gida Hajiya ta rika yi mini godiya domin ta ji daɗin kunnenta. Tana addu'ar Allah ya raya mini ƴaƴana ya yi musu albarka, yaya Baffa ya yi murmushi ya ce,

"Hajiya ki fara roƙa mata miji na gari kafin ƴaƴa."


Ta ce "Allah sarki! Sun rabu da mijin ne ko rasuwa ya yi?"


Ya ce "Bata taɓa aure ba."


"Me yasa?" Daddyn Khausar ya ambata a ruɗe.


Na yi ƙasa da kai hawaye na zubo mini, yayin da na tsinci muryar yaya Baffa na fad'in "Ƙaddararta ce. Ƙila kuma ba a hallici wanda zai so ta ya aure ta ba ne."


"An halitta; ina son ta; kuma zan aureta." Daddyn Khausar ya ambata yana kallona. Maganarsa ta janyo katsewar numfashina na wucin gadi.*******


Sunana Binta Jibril, mu biyu kacal iyayenmu suka haifa; ni da yayana Abubakar da nake kira yaya Baffa. Gidanmu gida ne na gandu da yake ɗauke da sassa daban-daban na yayyen mahaifina da ƙannensa. Mun ta so da ragowar sa'annina kuma ƴan uwana na dangi. Amma har muka girma muka isa aure babu wani namiji da ya taɓa furta mini kalmar so; duk da kasancewar ina da kyawun halitta fiye da ƴan uwana. Wannan ya janyo mini karan tsana daga mutanen gidanmu har ma da mahaifina. A wajen mutane biyu kawai nake samun sauƙi wato mahaifiyata da yayana; har aka aurar da ƙannen bayana ban dace da mashinshini ba. Idan ina kuka mahaifiyata ke rarrashina; idan dare ya yi ta kan hana kanta barci ta yi ta salloli tana mini addu'ar samun miji na gari. Mahaifina kuwa ban da miyagun kalamai da cin zarafi babu abin da yake shiga tsakanina da shi, mahaifiyata ta sha yin kuka tana roƙonsa akan ya sassauta mini tunda ba laifina ba ne daga Allah ne; amma ya gaza fuskantar hakan.

Ina da shekaru talatin da uku, watarana na wayi gari da bunƙasar ƙaddarata. mahaifina ya yi rantsuwa tunda ba zan nemo miji na yi aure ba to sai na bar masa gidansa; ko ma ina ne na tafi ba shi da asara. Ina kuka haka ya rabani da uwata ya dinga jefo mini kayana tsakar gida; jama'a suka taru suna kallo amma babu wanda ya yi yunƙurin dakatar da shi. A lokacin ne yaya Baffa ya shigo ya iske wannan tashin hankali, na ɗibi gudu na afka ƙirjinsa ina wani irin kuka kamar na shiɗe.


"Yaya Baffa don Allah ka nemo mini mijin aure. kuturu, makaho, bebe, kurma, ko wanda ya haɗa dukkan waɗannan nakasar ina so zan aure shi. Ko don na yi haske a idanuwan mahaifina."


Ɗumin hawayen yaya Baffa da ya sauka a dokin wuyana ya saka ni ɗagowa na dube shi "Faɗima! Wallahi da Allah ya halatta aure tsakanina da ke da a yau zan aure ki; sai dai akwai babban shinge tsakanina da ke, ki yi haƙuri Allah yana tare da ke. Ni ma ina tare da ke."


A ranar Yaya Baffa ya ɗauke ni daga gidanmu zuwa gidansa; mahaifiyata ta umarce shi akan ya yi mini duk wani gata kada ya bari hawayena ya ci gaba da zuba. Na fuskanci ƙalubale a zamana gidansa saboda matarsa ta ɗora mini karan tsana, ta wahalar da ni har zuwa lokacin da ya ankara; daga nan suka samu matsala har ta yi furucin sai dai ya zaɓa ko ni ko ita, a take ya zaɓe ni ya barta.


Duk wata hidima ta karatuna yaya Baffa ya tsaya mini, a haka na jure wa ƙaddarata na dage da neman ilimi domin kar na yi biyu babu. Har zuwa lokacin da na kammala karatu na zama cikakkiyar likitar ido da kunne.

Ranar da na kammala karatu yaya Baffa ya umarce ni domin na je na duba Ummata ba ta da lafiya, mahaifina ya yi mini korar kare, wannan ya ƙara rura lalurar Umma ta rasu a ranar bayan fita ta da awa ɗaya. Na yi kuka tamkar hawayena za su ƙare, kuma har yanzu ban daina kukan rashin mahaifiyata ba. Yaya Baffa shi ya zame mini garkuwa har na kai matakin da nake a yau. Duk da har zuwa yanzu babu namijin da ya taɓa duba na ya furta mini kalmar so. Sai Daddyn Khausar.


********


Tunanin rayuwata ya katse a lokacin da yaya Baffa ke shai da mini an ɗaura aurena, hawaye ya tsinke mini na farinciki. Wannan rana ta riske ni BA ZATO!


"Allah ya jiƙanki mahaifiyata, ina ma kina raye kiga wannan rana." Na ambaci hakan.


Da yammacin ranar kafin na tare a gidana na yi wa mahaifina aikin ido, sakamakon makancewa da ya yi. Kwana biyu da hakan muka iske shi ni da mijina idanuwansa sun buɗu, yana ganina ya fashe da kukan nadama; yana roƙon gafarata. Sai ni ma na kama kukan, a yayin da na ɗago kai na ga hannuwa guda uku suna miƙa mini yanki domin na goge hawayena; hannun yaya Baffa, hannun Khausar da hannun mijina Alhaji Ahmad Mai Dala. Da na rasa na wa zan karɓa; kawai sai na sakar musu murmushi.


Ƙarshe!

Reactions
Close Menu