Karanta 'Sarauta Ko Zalunci' Gajeren Labari

Labari mai jigo a kan mulkin zalunci

___________________________________________________________________________________

RUBUTAWA KARIMATU ABDULHAMID

       ( MUMMYN MINAL)

FARKO

Gudu sukeyi sosai suna ratsa gonaki amma sai binsu akeyi, idan sun juyo sunga ana binsu sai suk'ara k'arfin gudunsu. Amamaki na macece da namiji suke wanan gudun, kuma macen tsohon ciki ne ajikinta! Suna cikin wanan gudun macen tafad'i a k'asa tana Nishi da k'ar, duk'awa namijin yayi agabanta ya kamo hanunta cikin wahala da gajiya yace " Tabawa ki tashi mutafi muci gaba da gudu har mubar nahiyar nan kar domin idan mugayen mutanan suka kamamu ba k'alemu za suyi ba har sai sun kaimu gaban Sarki mark'udu"


Cikin wahala da k'arfin hali Tabawa tace " A'a Megida na kawai kaje abunka ka k'aleni ni nasan mutuwa zanyi anan gurin saboda haka kawai ka tafi ba naso su kamaka domin sarki Mark'udu kasheka zaisa ayi"


Ya bud'e baki zaiyi magana Kenna ya hango mutanen da suke binsu sun kusan cinmusu, hannuwansu rik'e da mugayen makamai, kawai zama yayi agaban matartasa yana kuka yana cewa "abun bauta ka taimakemu ka tsaratar damu daga zalincin Sarki mark'udu"


Kafin suyi wani yunk'uri tini mugayen da suke binsu suka zagayesu, acikin wani ya d'aga k'arfe ya kwad'a mar akansa, ai kuwa sai jini yayi tsirtuwa ya fara zuba, shiko tini ya baje agurin asume, itako Tabawa hannunta ta d'aura akanta tana cewa karku kashemin megidana. Abun bauta kataimakemu"


Amma ina ko su kulata haka suka sa igiya suka d'aure k'afafuwansa suna jansa acikin gonaki, duk jikinsa yayi jina-jina ko ina ya wanke da jini ajikinsa domin kuwa k'ayoyi duk sun sassokeshi ga duwatsu da suke jansa akansu suma duk sun jimar ciwo.


Itako Tabawa itama gudu takeyi tana kuka tana binsu abaya, abun da ke cikin ta kuwa ji takeyi tamkar zai tsagata ya fito saboda wahala, amma ina ita tamijinta takeyi, ahaka suka shigo wani babban gari, inda mutane kowa sai binsu da kallo akeyi yana basu hanya domin kowa yasan mutanen Sarki mark'udu ne, kuma ba wanda ya isa ya tanka sai de uwarsa ta haifi wani, masu d'an tausayin ciki ne suke matse hawaye.


Ahaka wa 'yanan mugayen suka shiga fadar garin da mijin tabawa wanda ko motsi bai iya yi, itama kuma Tabawa tana biye dasu tana gudu da k'ar.

Suna shiga tsakiyar fadar aka fara k'irari da cewa " barka da zuwa fadar sarki Mark'udu uban masu taurin kai sarki mai ji da mulki da izza, ina maza to ga Babanku, maza sunja dakai sunbarka Sarki mark'udu gagara badau d'an Jagiru, ina Wanda yace da shi ba shi ba, uwarsa ta haifi wani, ta ko ina sautin wanan k'irarin shi yake fita afadar, ga wasu manya- manyan gumaka akewaye a fad'in Fadar muddin ka d'aga kai ba'a bunda zaka gani sai gumaka sanan ba'ajin sautin komai acikin fadar sai sautin k'irarin da ake yiwa Sarki mark'udu, bayi kuwa marasa galihu sai aikin bauta sukeyi acikin fillin fadar, ga wasu mugayen mutane da manyan bulali ahanunsu suna bin wa'yanan bayin duk Wanda baya aiki da kyau saide yaji sauk'ar dukka mai firgitarwa ajikinsa.


Tafiya kad'an wa 'yanan mugayen mutanan da suke jan mijin tabawa suka k'ara acikin masarautar, suka iso gaban Sarki mark'udu, wanda yake zaune akan kujerar sa yana ta narkar giya mai tsami mabiyansa kuwa suna kewaye dashi suna ta zabgamasa k'irari da yakarad'e fad'in fadar, suna isa gabansa sukayi wulli da mijin tabawa gefe, sanan suka ce " sarki Mark'udu gagara badau uban maza, ga d'an banzan nan munkawo maka"

Sarki mark'udu kuwa bud'e bakinsa yayi me kama da band'akin makarantar firamare ta gwamnati saboda k'azantar sa, da d'oyinsa dariya yayi Hhhhhhhhhh sanan yace "


Mu had'u a shafi na biyu

Reactions
Close Menu