Karanta 'So Halitta Ne!' Gajeren Labari

Labari a kan soyayya mai wahalarwa

__________________________________________________________________________________SO HALITTA NE

Na

Naanah M. Sha'aban

Farko

Babbar makaranta ce wadda take d'auke da yammata da samari, kowa sai zirga-zirgarsa ya ke yi a cikin makarantar da alama an fito break ne, wata budurwa na ga ta fito daga cikin wani aji tana tafiyarta cikin nutsuwa sanye take da uniform kamar sauran d'alibai, tayi tafiyar kusan minti 30 sannan na ga ta shiga wani aji bakinta d'auke da sallama "Assalamu alaikum" Wani kyakkyawan saurayi ne a cikin ajin shi kad'ai ga littafi a hannunsa yana karatu, bai d'ago ya kalleta ba kuma bai amsa sallamar da tayi ba, sai ma d'aure fuska da yayi tamkar bai tab'a yin murmushi ba, kwata-kwata ba ta damu da rashin amsa sallamar da bai yi ba sai ma murmushi da tayi ta k'arasa har gudun da yake zaune tare da kiran sunansa "Ahmad" Nan ma bai d'ago ba sai ma tashi da yayi zai fita daga ajin ta rik'e gefen rigarsa tare da cewa "Ahmad meye laifina dan na ce ina sonka kuma ai"....Cikin tsawa ya dakatar da ita da cewa "Ya isa Aiman ki ke da suna ko wa? Ba na buk'atar soyayyar ta ki, ki je ki rik'e dan ni wallahi duk duniyar nan babu wacce na tsana a rayuwata sama da ke, ki fita a rayuwa" Nan ya tashi a fusace zai bar ajin, ta rik'e masa gefen riga idanuwanta suna zubar da hawaye "Dan Allah Ahmad ka".... Saukar zafafan marin da ya gere mata guda biyar ne yasa ta kasa k'arasa abin da take shirin cewa, ta saki rigar ta sa, ta dafe kuncinta da hannunta tana kuka, shi kuwa ya fita fuuuuu! Kamar kububuwa yabar ajin.


Durk'ushewa tayi a k'asa tare da rushewa da wani irin kuka "Wannan wace iriyar k'addara ce, meyasa zuciyata za ki yi min haka, me nai miki zaki dora min son wanda kwata-kwata a rayuwarsa ya tsane ni" Ta k'arasa maganar tare da fashewa da wani matsanancin kuka mai sosa zuciya, "Iman ki yi hak'uri na san irin yadda ki ke ji, amman ya kamata ki hak'ura da Ahmad dan shi sam bakya gabansa ya kamata ki san da haka, dole ki yak'i zuciyarki ki rabu dashi, Ahmad ba ya sonki kuma ba zai tab'a sonki ba, ki duba fa irin abin da yayi miki jiya a gaban Mommy da Abba wannan ma kad'ai ya isa yasa ki rabu dashi kuma ki san ba zai tab'a sonki ba" Da sauri Iman ta d'ago kanta su ka yi ido biyu da K'awarta Meenart wacce take tsaye a gabanta ta zuba mata kyawawan idanuwanta, tsugunnawa Meenart tayi kusa da Iman suna fuskantar juna, Iman ta ce "Besty tabbas na san Ahmad baya sona amman kuma ban fitar da rai ba nasan wata rana Ahmad da kan shi zai zo ya ce min yana sona, kuma ya ba ni hak'uri a kan abin da yayi min" Meenart tayi wani murmushi me ciwo tare da cewa "Ai kuwa indai ba za ki cire Ahmad a ranki ba kina tare da wahala, mutumin da zai kalli idanuwan Iyayenka ya ce musu su fad'awa mahaukaciyar 'yarsu cewar baya sonta, ko kin manta ne shin bakya kishin Mommy da Abba ne?, ni kai na da ba ni ya fad'awa wannan maganar ba, na ji matuk'ar ciwon maganar" Iman ta ce "Nima na ji ciwo, amman babu yadda zan yi domin son Ahmad a cikin jini na yake ba zan iya cireshi daga raina ba","Hmmm! Iman dole nayi miki uzuri domin kuwa kin fad'a mahaukaciyar soyayya" Meenart ta fad'a tare da mik'ewa tsaye,ta fara tafiya cikin nutsuwa "Meenart karki manta So halitta ne, Allah ne ya halicci son Ahmad a cikin zuciyata kuma ina ji a jikina idan har ban samu Ahmad ba mutuwa zai yi, ba zan tab'a iya rayuwa ba tare dashi ba" Tana kuka ta ke yin maganar tana jin zuciyarta tamkar zata faso k'irjinta, Meenart ta juyo tana kallonta, ita kam lamarin Iman gaba d'aya haushi yake ba ta, ji take tamkar ta je ta rufeta da duka "Malamar soyayya idan kin gama kukan za ki iya zuwa mu tafi gida" Wata iriyar ajiyar zuciya Iman ta sauke sannan ta mik'e jiri na d'ibanta har ta k'araso gurin da Meenart take tsaye, ta kama hannunta suka fita daga ajin, sun yi tafiyar kusan minti biyar sannan suka isa gaban wata mota wacce ka na ganinta kasan an zubar da kud'ad'e kafin a mallaki motar, suka bud'e murfin bayan motar suka shiga, Idi driver ya ja motar suka d'auki hanyar gida.


Suna isa tafkeken gidan wanda kallo d'aya za kai wa gidan kasan ba k'aramin mai kud'i ba ne mamallakin gidan, ta ko ina ya tsaru sai da mu ce ma sha Allah, Idi driver yayi wa mai gadi hon ya wangale musu babban gate d'in gidan, ya shiga gidan yayi parking a gurin da aka tana da don yin parking, Meenart da Iman suka fito daga cikin motar, Iman ta kama hannun Meenart sannan suka nufi hanyar da zata sada su da babban falon gidan, sun yi tafiyar kusan mintina hamsin sannan suka isa kofar da zata sadasu da falon, suna k'arasawa kusa da kofar ta bud'e da kanta suka shiga bakin su d'auki da sallama "Assalamu alaikum" Babu kowa a falon dan haka suka nufi 'bangaren Mummy, suna shiga suka tarar da Mummy zaune a kan kujera tana kallon labarai, sallama sukai mata tare da zama kusa da ita "Wash Mummy mun gaji da yawa" Meenart ta fad'a tare da kwantar da kanta a kan kafad'ar Mummy, "Ayya! sannu bari na kirawo Larai ta kawo muku abinci sai ku je ku yi wanka","A'a Mummy wanka zamu fara yi sannan mu ci abinci" Meenart tayi maganar cikin shagwab'a "To shikenan Yarinyata ku yi yadda ku ke so" Mummy tayi maganar tare da juyowa tana kallon Iman wacce tun shigowarsu ta samu guri ta zauna tare da zabga tagumi tana tunanin Ahmad, "Iman! Iman!!" Mummy ta kira sunanta har sau biyu amman sam Iman ba ta san ma tana yi ba, dan tayi nisa cikin tunaninta.


Meenart cike da takaici ta ce "Mummy ai ba za ta ji ki ba, tana tunanin wannan d'an iskan yaron mai kama da aljanu" Mummy ta mik'e ranta a 'bace "Allah ya kyauta" Abin da ta fad'a kenan, tare da shigewa bedroom d'inta, Meenart ma tashi tayi tare da k'arasawa gurin da Iman d'in take zaune ta yi mata dundu a baya, Iman ta d'ago a firgice tana kallon Meenart "To idan kin gama tunane-tunanen na ki sai ki zo mu je 'bangarenmu" Meenart ta yi maganar tana hararar ta, Murmushi Iman ta yi ba tare da ta ce komai ba, ta mik'e Meenart ta kama hannunta suka nufi 'bangarensu.


Wace ce Iman?

Fatima Musaddam shine asalin sunanta, mahaifinta shahararran Mai kud'i ne, a garin kano ita kad'ai ce 'yarsu, Meenart ta kasance 'yar k'anwar Mummy ce saboda irin shak'uwar da su ka yi da Iman yasa Mummy ta d'aukota tun tana 'yar shekara biyar, aka saka su makaranta lokacin da suka gama makarantar secondary school aka samar musu admission a school of nursing, suka fara zuwa a ranar kuma zuciyar Iman ta kamu da soyayyar Ahmad tun kallon da tayi masa na farko ta ji ya kwanta mata a rai, duk da kasancewar ba ajinsu d'aya ba, amman kullum sai Iman ta zo ajin tana rokonsa a kan ya kar'bi soyayyarta,amman shi kuma Ahmad ba shi da wani buri irin ya wulak'anta ta a gaban jama'a, duk makarantar babu wanda bai san irin son da Iman ta ke yi wa Ahmad ba, wasu suna tausaya mata, wasu kuma suna yi mata kallon mara hankali.


Ahmad iyayensa talakawa ne, shi kad'ai suka haifa d'an asalin garin jigawa ne, k'anin mahaifinsa ne ya d'aukosa lokacin da ya gama secondary school ya samar masa admission, Ahmad miskili ne ba shi da son hayaniya, yammata da yawa suna son shi amman saboda irin yadda suka ga yana wulak'anta Iman yasa kowacce shiga hankalinta, domin suna gudun wulak'anci da tozarcin da zai yi musu


Wannan kenan.


Zaune suke a kan taburma kowannansu da littafi a hannunsa suna karantawa Musaddik ya kalli Ahmad tare da kiran sunansa "Yaya Ahmad" D'agowa Ahmad ya yi yana kallonsa tare da cewa "Na'am k'anina" Musaddik ya ce "Yaya Ahmad meyasa ba ka son Iman? Ahmad ya d'aure fuska don shi ko sunan Iman ba ya so a fad'a a gabansa "Kaii karka k'ara yi min maganar wannan yarinyar","Yaya Ahmad na san ba ka son ayi maka maganar Iman amman ina son na fad'a maka cewa duk wanda ya furta yana sonka, to ya gama yi maka komai, dan ya fi mak'iyinka kuma wallahi Yaya Ahmad idan har ka bari Iman ta kub'uce maka to ba na tunanin zaka samu wacce za ta yi maka irin son tayi maka" Musaddik yana gama fad'ar haka ya tashi ya shige d'akinsa, Musaddik d'an Malam Hamza ne wato k'anin mahaifin Ahmad, Ahmad ya yi shuru na d'an tsawon lokaci yana nazarin maganganun Musaddik sannan ya cigaba da karatunsa zuciyarsa tana raya masa abubuwa da yawa.


"Abban Iman wallahi ni yanzu abun Iman tun yana ba ni haushi, har ya zama yanzu tausayinta na ke ji, saboda ta kamu da son yaron da sam shi ba ta ita yake ba, gaba d'aya ta rame ta lalace" Cewar Mummy da take zaune kusa da Abba tana zuba masa abinci, Murmushi ya yi tare da cewa "Tabbas nima ina tausayinta kuma, yanayin da take ciki yanzu yana matuk'ar ta yar min da hankali, da ace kud'i zasu iya siyan soyayyar Ahmad to da tuni na siyawa Iman" Mummy ta ce "Nima Abban Iman, dan wallahi hankalina yana tashi a duk lokacin da na ga Iman tana cikin damuwa ko tana tunanin wannan yaron" Abba ya ce "Addu'a zamu ta ya ta da ita, dan yaron nan ba mutunci ne dashi ba, saboda irin soyayyar da Iman ta ke yi masa ne yasa kawai ban d'auki matakin abin da ya ce mana jiya ba"," Hmmm! Abban Iman Allah dai yasa mu dace kawai" Mummy tayi maganar cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa "Amin" Abba ya fad'a tare da fara cin abincinsa, da ya gama Mummy ta kwashe kwanukan ta kai kitchen, ta dawo suka cigaba da yin hirarsu ta duniya abin gwanin ban sha'awa.


7:00am


Sanye take cikin kayan makarantarta tayi kyau sosai kamar dan ita aka yi kayan, Kallon Meenart tayi wacce ita ma ta gama shirinta tana zaune a kan kujera tana latsa wayarta "Besty ki zo mu yi breakfast mu tafi makaranta" Iman ta yi maganar tana zama kusa da Meenart ta janyo center table d'in da aka cika musu abin da za su yi breakfast da shi, ta fara bud'e wani babban kwanon kas, soyayyen dankali ne da kwai ta fara zuba musu dankalin a plate "Wato sister ke kawai so ki ke mu je Makaranta ki ga Ahmad ko? Wallahi besty ni har na fara jin tausayinki dan wannan d'an iskan ba lallai ya so ki ba, Amman zan ta ya ki da addu'a Allah ubangiji yasa ya so ki" Iman ta kalli Meenart ta d'an yi murmushi " Amin nagode besty, ni kai na ina tausayin kai na, ban san meyasa zuciyata tai min haka ba"," Besty yau fa ni ba zan je makaranta ba" Meenart tayi maganar tana ya tsine fuska "Meyasa ba za ki je ba? Kuma ai na ga kin saka uniform" Meenart ta ce "Wallahi tun da safe na ke jin cikina yana min ciwo, na so na je karantar amman na ji ba zan iya zuwa ba" Iman cike da tashin hankali ta ce "Subhanallahi shine ki ka yi shuru, tashi muje asibiti" Murmushi Meenart ta yi "Ba wani ciwo ne sosai ba, karki manta fa lokacin makaranta ya yi, gwanda ki je ki ga Ahmad kar yau mu tafi emergency" Dariya sosai Iman ta yi "To na ji, kin tabbatar dai babu matsala ko?" Meenart ta ce "tabbas" Iman ta d'auki jakarta tare da kissing d'in Meenart ta kunci ta ce "ki kula dear" Murmushi kawai Meenart ta yi mata, Iman ta fita da sauri babban falo ta nufa inda ta tarar da Mummy da Abba, nan take fad'awa Mummy Meenart ba ta da lafiya ba za ta iya zuwa makaranta ba, sannan tayi musu sallama ta fita da sauri dan ta san yanzu Idi driver yana jiranta a waje, Mummy kuwa 'bangarensu suka nufa ita da Abba domin duba jikin Meenart.


Ita kuwa Iman tana fita Idi driver ya bud'e mata mota ta shiga, ya shiga mazaunin driver ya ja motar mai gadi ya wangale musu gate suka nufi makarantar, suna isa Iman ta fito daga cikin motar ta nufi ajinsu, tana shiga Malami ya shigo ya fara yi musu lecture, bayan an tashi kamar kullum Iman ta nufi ajin su Ahmad tana zuwa ta tarar dashi shi kad'ai ga littafi a hannunsa yana karatu "Assalamu alaikum" Ta yi sallama tare da k'arasawa gurin da yake "Wa'alaikumussalam" Ahmad ya amsa sallamar ba tare da ya kalleta ba, Iman ta yi mamaki sosai dan tunda Ahmad bai tab'a amsa sallamarta ba "Ahmad gurinka na zo" D'agowa ya yi yana kallonta fuskarsa a murtuke sai kuma ya yi murmushi tare da cewa "Iman gani to" Wani irin farin ciki ne ya ratsata tare da cewa "Anya Ahmad d'ina ne wannan kuwa?" Ta yi maganar tana murmushi "Eh mana chanza miki nayi ne","A'a baka chanza min ba, dan Allah ina son rokon wata alfarma a gurinka" Ahmad ya ce "Ina jinki","Ahmad dan Allah ina son ka so ni ko da"... "Iman ina sonki dan Allah ki yi hak'uri da abin da nayi miki a baya, insha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba" Wasu irin zafafan hawayen farin ciki ne suka shiga zubowa daga idanuwanta, ta ma rasa abin da zata ce masa dan kuwa ji take kamar ta zuba ruwa a k'asa ta sha, durk'ushewa ta yi a gabansa tana kuka "Tabbas yau ita ce ranar da ba zan tab'a mantawa da ita ba a rayuwata, ina sonka sosai" Wani farin handkey ya d'auko a aljihunsa ya mik'a mata, karb'a tayi ta shiga goge hawayen fuskarta dashi "Ki tashi kukan ya isa haka, idan kuma ba so ki ke nayi fushi ba" Ta mik'e tana murmushi "to na daina kukan, zan tafi gida Idi driver yana jira na" Ahmad sai da ya rakata har wajen motar, ta shiga Idi driver ya ja motar suka nufi hanyar gida, handkey d'in da Ahmad ya ba ta ta rumgume shi tare da lumshe idonta, tana k'ara jin son Ahmad yana shiga zuciyarta.


Suna isa gidan, Iman ta nufi cikin gidan da gudu tana shiga ta tarar da Meenart tana kallon wani indian film, jikinta ta fad'a "Besty yau Ahmad ya ce yana sona" Meenart ta ce "Besty da gaske ki ke, Ahmad ya ce yana sonki" Iman ta rumgumeta sosai "Wallahi sister wannan ma handkey d'in shine ya ba ni","nayi murna Besty" Meenart tayi maganar tana jin dad'i burin bestynta ya cika, Iman zuciyarta farin ciki ya gama cikata.


Alhamdullahi anan na kawo k'arshen wannan labari!

Reactions
Close Menu