Wa ya cancanci yabo: marubuci ko darakta?

Tare da Nasir Kainuwa Haɗejia


A kwanakin baya ina kama wani gidan rediyo sai na ji ana magana akan shirin fim ɗin Labarina, amma sai na ji gabaɗaya an kwashe romon fim ɗin an ba wa Darakta (Aminu Saira), Marubuci (Ibrahim Birniwa) kuma ko oho domin ko sunansa ban ji an kama ba. 


Wasu fa a wajensu marubuci ba komai ba ne, Darakta shi ne komai. Duk girman Darakta duk isar sa marubuci ne gatansa, ba  wai ga fim na Hausa kaɗai nake magana ba har ga fina-finai na Indiya, Amurka da dai sauransu.Marubuci ana iya faɗa masa kalma ɗaya ya rubuta littafi mai shafi dubu a kanta, marubuci ana iya faɗa masa kalma ɗaya ya rubuta SERIES FILM a kanta. Amma da zarar fim ya fita ba kowa ke ganin ƙoƙarin marubucin ba. Sai dai a jinjinawa Darakta da kuma jaruman cikin shirin. Marubuci shi ne komai a fim domin in marubuci bai rubuta labari ba darakta ba zai bada umarni ba, shi kuma jarumi ko mu ce tauraro yana jiran umarnin abin da zai aiwatar ne da ga wajen Darakta, a saboda haka jarumi na rawa ne da bazar wanda yake rawa da bazar marubuci. Ya kamata dai marubuta su yi rubutukan da za su fito da kimarsu da kuma martabarsu, yadda za a fahimci irin kokarin da suke wajen samar da labarai.Darakta ke bada umarni, amma kuma shi marubuci ne ke ba shi umarnin da zai bayar. Marubuci shi ne zuciyar fim, abin da ya saƙa da shi ake amfani ko da kuwa wajen haska fim an ranƙwashi labarin, hakan ba ya sa a ce  an bar turbar da marubuci ya ajiye labari. Duk da haka ba wai na kushewa Daraktoci ba ne, a'a ina so na nuna yadda marubuta ke da bakin magana ne. 


Marubuci da Darakta Ɗanjuma ne da Ɗanjummai kowanne na ƙarfafar ɗan uwansa, amma na fi martaba marubuci. Marubuci tamkar magidanci ne, da zai fita ya nemo abinci ya kawo gidansa, a girka. Komai iya girkinki in mai gida bai kawo ba dole ki haƙura. Komai shahara da ƙwarewar Darakta in ba a rubuta ba dole ya haƙura.


Nasiru Kainuwa Hadejia
08100229688
Reactions
Close Menu