Baƙin fata ya lashe kyautar gwarzon marubutan duniya ta "Nobel Prize"

Abdulrazak Gurnah wanda ya kasance haifaffen ƙasar Tanzania ne, ya zamo gwarzon da ya samu damar lashe kambun "Nobel Prize" a ɓangaren rubutu sakamakon rubutun da ya yi game da rayuwa bayan mulkin mallakar turawa da kuma halin da ‘yan cirani, masu gudun hijira ke tsintar kansu a ciki, nasarar da ta ba shi damar zama ɗan Afrika na 5 kenan da ya taɓa lashe kyautar ta Nobel a ɓangaren rubutun adabi.
An haifi Abdulrazak Gurnah ne a ƙasar Tanzania ranar 20 ga watan Disamban 1948, cikin wani yanki da ake kira Zanzibar gabannin komawarsa Ingila a shekarar 1968 a matsayin ɗan gudun hijira. Inda a nan ne ya samu damar fara karatun sa a cikin ƙasar gabannin kaɗawar guguwar juyin juya halin yankin na Zanzibar wadda ta kai ga kuɓucewar ikon yankin daga hannun larbawa wanda kuma ya haddasa kwararar tarin ‘yan cirani zuwa sassan Duniya.


Gurnah ya ci gaba da karatu a kwalejin Chris Church da ke karkashin jami’ar London inda ya samu digirin farko.


Gurnah ya kammala PhD a shekarar 1983 inda ya yi koyarwa a Jami’ar Bayero da ke Kano a Najeriya tsakanin shekarun 1980 zuwa 1982.


Har zuwa lokacin ritayarsa, Farfesa Gurnah ya ci gaba da aiki da jami’ar Kent inda ya yi aiki tare da fitattun marubuta na Duniya ciki har da V.S Naipaul da Salman Rushdie da kuma Zoe Wicomb yayinda ya taka muhimmiyar rawa a mujallar Wasafiri tun daga 1987.


Gurnah na daga cikin jerin farfesoshin Afrika da suka kware a rubutun Zube inda ya yi rubuce rubuce masu muhimmanci da suka kunshi Paradise a 1994 da kuma Desertion a 2005 kana By the Sea a 2001 littattafan da dukkaninsu ya samu lambar yabo a kansu.

Reactions
Close Menu