Shin Ko Kun San Mece Ce 13x13 Da Manufarta?

...an kafa wannan yunquri ne da manufar dago da masu fasaha da masu baiwa, daga mawaqa, marubuta jaruman fim, yan wasan kwaikwayo ko dago da darajar wadannan masu fasaha a kowane fage na basirar da Allah Ya ba su a siyasa ko waqen al'uma ko wa'azi ko don harshe wato adabi a dunkule.

Shin Ko Kun San Mece Ce 13x13 Da Manufarta?

Tare da Hashim Abdallah

Daga masu son shigarta, har zuwa kan masu rarraunar fahimta gare ta da masu neman fahimtar mece ce ko kuma dalilan adafin sunanta da sha'uku-sha'uku, duk ku bude kunnuwanku.

Jagorori a cikin tafiyar 13×13 na matakin ƙasa kuma waɗanda suka kafata


Ma'anar 13x13 Thirteen-Thirteen ko in da Hausa ne, wato sha'uku-sha'uku.


Kungiya ce samarwar mutane 13. Hakika kuma Alkhairi ne, kamar yadda taken tafiyar yake, da aka yi imani zai 'yanta 'yan Najeriya domin samar da rayuwa mai inganci ko inganta rayuwar ta fuskoki daban-daban gaba da siyasa ko wakar siyasa ko kamfe. Ba ta da wani makiyi sai makiyin al'uma. A dalilin hadafi na 'yanta kasa, lallai 13x13 ta kafu ne mahadi-ka-ture wato har illa mashaAllahu.


Wato an kafa wannan yunquri ne da manufar dago da masu fasaha da masu baiwa, daga mawaqa, marubuta jaruman fim, yan wasan kwaikwayo ko dago da darajar wadannan masu fasaha a kowane fage na basirar da Allah Ya ba su a siyasa ko waqen al'uma ko wa'azi ko don harshe wato adabi a dunkule. Yunkurin na da manufar nuna kimarsu ko irin rawar da suke takawa ko za suke takawa fiye da gaban a aikin fasahar ko bayan wannan baiwa, abubuwan da suka hada da neman cigaban al'uma kuma domin tallafa wa al'umar da ciyar da ita gaba, bisa jagorancin manyan mawaqa da sauran masu fasaha da basira da kafatanin masu ruwa da tsaki a wannan fagage da aka ambato. Tafiyar harkar nau'ukan adabi domin adibai da janibinsa.


Yana da muhimmanci mu fahimci tafiyar ba ta siyasa ba ce, kuma tafiyar ta siyasa ce domin akwai tunanin ceto qasar da fafutukar samuwar shugabanni nagari a kowacce jam'iyya kuma bisa yarjejeniya da fafutukar talakawa da yarjewarsu domin ake cika musu alkawari da samar da shugabanni nagari, domin wayar da su domin wayar da su kan manufofin nusar da su muhimmanci irin nasu, a matsayin gudumawar mawaka.


Wannan kungiya tana da shugabanci, Kuma shugaba na kasa shi ne, Dauda Kahutu Rarara da Kwamitin gudanarwar jihohi na kasa karkashin babban mawaki ElMu'az Birniwa. Babban marubucin fina-finai Ibrahim Birniwa ya zama mataimakin shugaban kwamitin siyasa na kasa Ibrahim Birniwa, yayin da shugaban shirye-shirye, kuma mataimakin babban manaja na gidan talabijin na Arewa24 Rabiu Gumel ne shugaba reshen jihar Jigawa.


Sannan kuma wadannan jigogi 13 sun hada da:

1, Dauda Kahutu Rarara

2, Aminu Ladan Alan Waka

3, El'muaz Birniwa

4, Adam A Zango

5, Ali Jita

6, Umar M Sharif

7, Yakubu Muhammad

8, Daddy Hikima (Abale)

9, Kamilu Koko

10, Baban Cinedu

11, Nura M Inuwa

12, Aisha Humaira

13, Abubakar Bashir Maishadda


A halin yanzu akwai rassa su ma masu mukamai 13 a jihohin:

Kano

Kaduna

Jigawa

Katsina

Gombe

Kebbi

Niger

Birno

Adamawa

Plateau

Nassarawa, da sauransu.


Yana da kyau mu kara fahimtar cewa, a kowacce jihar akan samu mutane fasihai kuma adibai da jaruman fim a matsayin shugabanni ko mambobi, gami da mawakan yabon Annabi (S) inda a Kanon Dabo jigon waken Annabi, Mal Bashir Dandago. Abin dai gwanin ban sha'awa.


Wannan yunkurin dai na kungiyar 13x13 yana da taken "Alkhairi ce" kuma akwai niyya da nufin karade Najeriya inda ko a kudu an ba da karfin farawa da Fatakwal (Port Harcourt). Yunkurin na da manufar tallafa wa masu karamin karfi da tallafa wa marayu da gajiyayyu da mutan gidan yari. Akwai tunanin mafita ga kasa, musamman ta fuskar samar da tsaro dawwamamme, a hannu daya da tallafa wa 'yan kungiyar zuwa kan al'uma ta fuskar rage radadin talauci.


Yunkurin ba ruwansa da jam'iyya sai dai ya duba dan takara nagari domin mulkar jama'a.Hashim Abdallah

Sakataren 13x13 na jihar Jigawa

Reactions
Close Menu