KOWA YA KWANA LAFIYA... LABARIN RAHAMA SABO USMAN

KOWA YA KWANA LAFIYA...

                 Rahama Sabo UsmanGABATARWA

A shekarar 2021 da ta gabata ne ƙungiyar Arewa Media Writers reshen Jihar Filato ta shirya wata gasar marubuta ta Gajeren Labari da Insha'i ƙarƙashin jigon FARFAƊO DA KYAWAWAN AL'ADUN AREWA DON INGANTA TSARO DA ZAMAN LAFIYA, wanda ta kasance irin ta ta farko da wata ƙungiyar marubuta ta shirya a Jihar Filato, wacce ta ƙunshi marubuta maza da mata da suka fito daga sassan Nijeriya da ƙungiyoyin marubuta daban daban. Labarin KOWA YA KWANA LAFIYA.. na Rahama Sabo Usman daga ƙungiyar First Class Writers Association da ke Jihar Kano shi ne ya zo zakara a mataki na farko a gasar. Za mu ci gaba da kawo muku jerin sauran taurarin labaran da suka yi fice a gasar, don amfana da darussan da labaran ke koyarwa.

*****                        *****                       *****

FARKO

Jini ne ke malala ta ko'ina, sassan jikin ɗan Adam a zube tamkar guntayen biredi a kan juji. An ƙawata ƙasar gurin da jinin bil'adama tamkar gurin da a ke yanka dabbobi a mahauta (kwata). Iface-ifacen mutane ke tashi cikin yanayi mai tsuma zuciya, hayaƙi ke tashi  ta ko'ina yana shigewa cikin giza-gizai, hakan sai ya mayar da sararin na subhana baƙiƙƙirin tamkar hadari  ya gangamo a tsakkiyar damina.

Wasu mutane masu kama da Samudawa  masu ƙirar ƙarfi, ke shiga gida-gida suna fito da mutanen ciki, a kan idon mai gida za su yi wa ƴarsa da matarsa fyaɗe bayan sun kammala kuma, su aika su ga barzahu ta hanyar yi musu yankan rago, mai gidan kuma su tura shi cikin gida daga ƙarshe su cinnawa gidan wuta.

Tsananin abin tausayi da ruɗa zuciyar dukkanin wanda ya ke da imani, wata mata ke tsananin gudu domin kaucewa ibtila'in ƴan tada ƙayar bayan, bayanta ɗaure da majanyi ta ƙulle wani abu tamau. Tsananin gunjin kukan da matar ta rusa ne, zai daɗa karyar maka da zuciya yayin da ta duba bayanta ta ci karo da abin da ta goyo, saboda ruɗewa da firgita a madadin ɗiyarta ƴar wata takwas ashe abin tada kai ta goyo. Nan take zuciyarta ta tsaya da aiki sa'ilin da ta juya ta hangi gidan da ta baro ɗiyar tata tuni ƴan ta'adda sun banka masa wuta. Kaico!

Garin Damau kenan mai ɗauke da ɗimbin al'umma, masu mabanbanta yaruka, al'adu, ɗabi'u da kuma addinai. Wannan bambanci ya haddasa ƙiyayya, gaba da kuma tarin ƙyashi da hassada wanda ya rikiɗe zuwa ga faɗace-faɗace maras tushe balle makama da sunan kare martaba da kiyaye addini.

Allah ɗaya gari bamban duk da tarin rashin tsarki da zukatan mutanen wannan gari ke fama da shi, Allah ya ware mutum guda nagartacce mai hali da ɗabi'a mabambanciya da ta saura. Kullum burin wannan bawan Allah a haɗa kai domin a zamo tsintsiya maɗauri guda, yana da mace guda da kuma ƴaƴa samari guda biyu haɗi da tarin mabiya.

Kandagarki mai taken yakana, tun kafin yaran nan nashi biyu su kai munzali ya kwashe su ya tura su birni, gurin wani ƙaninshi don su koyi ƙwadago su kuma azurta da samun gishirin rayuwa, wato ilimi. A ƙasan zuciyarsa kuma yana jin tsoron kada su tashi a garin su koyi zalaƙar zubda jinin bil'adam. Haƙonsa kuwa ya cimma ruwa, don sun samu nagartaccen ilimi daga firamare har zuwa digirewa a kan ilimin lauya.

Cikin alfahari da tinƙaho suka dafo zuwa garinsu, wanda mahaifinsu ya yi musu katangar ƙarfe da shi na tsawon shekaru. Burinsu shi ne su gwadawa mahaifin nasu yadda rayuwarsu ta juya daga ƙasa zuwa sama, su kuma yi arba da kykkyawar fuskar da suka jima ba su yi tozali da ita ba sanadin sadarwa da ta yanke a tsakaninsu na tsawon watanni.

Tsautsayi da ba a ba shi wa'adi, burinsu na arba da mahaifinsu ya juya ciki domin dirarsu garin ke da wuya, labarin kisan gillar da aka yi wa mahaifinsu ya iso ga kunnuwansu. Alwashi suka ɗauka na sai sun maido da jinin mahaifansu da ya malala a ƙas, tarin makaman da mabiya mahaifin nasu suka tara don jiran irin wannan rana suka hau jida suna faman ihu da faganniya. Rayukansu tamkar ɗan budan da a ka zaro daga maƙera. Masu fushi da fushin wani suka dafe musu baya suna kururuwar neman ɗaukar fansa. Kai tsaye cikin gari su ka yi wa tsinke!

Jini ya fi ruwa kauri. Kafin su yi wata ƙwaƙƙwarar tafiya, babban yaron malamin mai suna Mustafa jikinsa ya sanyaya, wani ɗan ƙaramin tunani ya zo masa a rai, yanzun yadda mahaifinsu ya yi gwagwarmayar a zauna lafiya za ta faɗi a banza kenan? Tunda su yaranshi sun gaza tallafawa burin shi bayan baya nan. Suna ƙoƙarin biyewa dokin zuciya mai linzami tamkar baƙin ƙarfe. 

Cak, ya tsaya da tafiya,"Ku dakata!" 

Ya faɗa cikin murya mai kama da amsa kuwwa.

Tamkar saukar aradu haka muryar tashi ta isa ga kunnuwan sauran mabiya, ba tare da shiri ba suka ja tunga don cika umarni.

Cikin gwanancewa a sarrafa harshe ya fara bayani, "Bai kamata mu riƙa rayuwa irin ta dabbobin ruwa ba, kamata ya yi mu rayu tamkar tsuntsu a cikin sheƙa. Zubar da jini laifi ne a kowanne addini. Babu wani littafi da aka saukar wanda ya ke nuni da mutane su yaƙi junansu ba. Bal, ma littattafan da dama sun sauka suna nuni da zallar munin da ke cikin zubar da jinin bil'adam. Kada mu ƙawata ƙasarmu da jininmu ko na ƴan'uwanmu babu fa'ida a gurin kashe rayuka. Sai ma tarin hasara da taɓewa mabayyaniya. Idan har muka ɗaga makami da niyyar yaƙi, ƙarshensa shine mu kashe ko a kashe mu, kuma cikin wannan yaƙi dole mu kashe wanda bai ji ba kuma bai gani ba. Shin wacce riba za mu tsira da ita idan mun yi hakan? Babu".

Amsar da ya ba wa kansa kenan, ganin sun yi shiru babu mai ƙwaƙƙwaran motsi da alama saƙon nashi na zuwa gurin da ya ke buƙata. Don haka cikin karsashi da tarin ƙumaji ya ɗora.

"Don haka daga yau ni da ɗan'uwana, za mu tashi tsaye mu kuma ɗora daga gwadaben da mahaifinmu ya mutu a kai, za mu kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan gari namu mai albarka."

Miƙa wuya ƙarshen yaƙi, cikin sanyin jiki mabiyan nasu suka hau zubar da makamai, cikin yanayi mai nuna mun ji kuma za mu yi biyayya. Jinjina ban girma suka hau yi wa zaratan samarin guda biyu, domin sun ga alamun cewar rigar da shugabansu ya ɗinka bai sanya ba ƴaƴan nasa na shirin saka masa.

Alƙawari kaya ne, kamar dai yadda su alƙawarta. Sun miƙe tsaye haiƙan gurin maida hankalinsu kacokam ga samar da zaman lafiya, da tsaro ta hanyar neman haɗin kan ƙabilu da addinai. Hakan ya sanya su jajircewa da halartar gurin dukkan wanda suka san shugaba ne na wani addini.

Hakan ya haska musu cewa babu wani shugaba da ke goyon bayan kisa da sunan addini ƴan bani na iya ne kawai daga magoya baya ke kiɗansu su kuma taka rawa abin su. Sun kuma basu tabbacin nuna goyon baya ɗari bisa ɗari ga wannan tafiya da su ka ɗauko. Kotun ta fi da gidanka su ka samar, mai taken 'Adalci Daga Matakin Farko' wacce ke hukunta dukkanin wata ƙabila da ke shirin tayar da rikici.

Shugaban ƙabilar da kanshi zai zaƙulo ko ma waye daga magoya bayanshi, ya miƙo shi domin a hukunta shi ko da kuwa ɗanshi ne. Dukkanin wani shugaba da ya yi biris da haka, za a tuɓe rawaninsa daga ƙarshe a bashi horo mai tsanani.

Dukkanin al'ummar da ke wannan yanki sun yi na'am da wannan sabuwar doka sun kuma yi rantsuwar za su yi mata biyayya sahu da ƙafa. Idan kuma lamarin ya ta'azzara ko kuma ya yi ƙamari za a damƙe koma waye sannan  a miƙa shi birni don jiran babban hakunci.

'Kowa ya kwana lafiya shi ya so!'

Mutanen garin Damau da ke yaƙi a kan ƙasarsu, yanzun sun mayar da ita ƙasar da su ke noma da kiwo. Kawunan ƙabilu da ya rarrabe a da a yanzun ya cure a guri guda, ko ƙifce da idanu babu mai yi ga ɗan'uwansa da sunan tashin hankali. Arziƙinsu ya bunƙasa darajarsu ta ɗaukaka.

Hakan ba ƙaramin kwarjini da tarin kamala ya sayawa garin nasu ba. Ga kuma tarin kuɗin shiga da su ke samu a kullum safiya da maraice, mutane daga sassa da dama ke ɓarkowa garin cin kasuwa, saɓanin shekarun baya da suka  shuɗe, wucewa ta gefen garin kan gagari al'umma. Duk shekara sukan haɗa bukukuwa ga masu al'adu daban-daban domin nishaɗi, soyayya da jin ƙai.

Lallai zama da lafiya ya fiya ya fi zama sarki kanshi.

ƘARSHE

Reactions
Close Menu