MAKIRCIN MASARAUTA... LABARIN ASMA'U ABUBAKAR MUSA

              Asma'u Abubakar Musa (Jasmine) 


GABATARWA

A shekarar 2021 da ta gabata ne ƙungiyar Arewa Media Writers reshen Jihar Filato ta shirya wata gasar marubuta ta Gajeren Labari da Insha'i ƙarƙashin jigon FARFAƊO DA KYAWAWAN AL'ADUN AREWA DON INGANTA TSARO DA ZAMAN LAFIYA, wanda ta kasance irin ta ta farko da wata ƙungiyar marubuta ta shirya a Jihar Filato, wacce ta ƙunshi marubuta maza da mata da suka fito daga sassan Nijeriya da ƙungiyoyin marubuta daban daban. Labarin MAKIRCIN MASARAUTA ... na Asma'u Abubakar Musa (Jasmine) daga ƙungiyar Manazarta Writers Association da ke Jos a Jihar Filato shi ne ya zo zakara a mataki na biyu a gasar. Za mu ci gaba da kawo muku jerin sauran taurarin labaran da suka yi fice a gasar, don amfana da darussan da labaran ke koyarwa.

******                         ******                      ******

"Wallahi ka faɗa min gaskiya a kan mugun abin da ka shuka da har ka ke firgice wa a cikin barci kana sambatu, idan ba haka ba sai na kai ƙarar ka gurin Mai Martaba tun da na fara fahimtar wasu daga cikin maganganun ka." Hadiza, matar Malam Naziru ke wannan zancen.

Tun yammaci da maigidan ta ya dawo daga Fada ta fuskanci cewa yana cikin tashin hankali, ko da ta tambaye shi bahasi bai bata amsa ba, hakan ya sa ta share. sai ga shi yanzu sam batun da yake yi a cikin barci sun farkar da ita.

Kalaman nasa sun sanya ta a cikin zargi duk da kuwa a cikin barci ya yi su. Hausawa suka ce, a san mutum a san cinikinsa. Mijin nata mutum ne mai matuƙar son abin duniya shi ya sa duk wasu mugayen aiki da ake gudanarwa a cikin Masauratar Joɗa yana da masaniya a kai.

Dalilin da ya sa ta tayar da shi daga barcin kenan don jin bahasi.

"Mugun mafarki ne fa kawai na yi, Hadiza. Kwanta ki ci gaba da barcin ki."

Ya faɗa yana kau da kai daga gareta, tun da dama ai mara gaskiya ko a kan doki yake sai ya yi ɗingishi."

"Shin dama kana da masaniya a kan waɗanda ke ta da husuma a wannan yankin ne?" Ta tambaya cikin mararin jin wata amsa daga gareshi, sai dai bai ce komai ba. Hakan ya sa ta cigaba da magana ta ce "Kuma shi ne ba ka sanar ba, ka bari ana ta asarar rayuka da dukiyoyi. Mugayen ɗabi'un naka har sun kai wannan munzalin?

Ba zan iya cigaba da zama da kai a haka ba." Ta ƙarashe maganar cikin zubar ƙwalla.

"Hadiza, wallahi a yanzu na yi nadama,
musamman abin da ya faru jiya ya matuƙar firgita ni. Ni da kaina yanzu na yanke shawarar tona asirin duk waɗanda muke wannan harƙallar da su."

Cikin zubar hawaye ya ƙarashe batun, hakan ya matuƙar bai wa Hadiza mamaki amma sai ta share tunda dai an ce labarin zuciya a tambayi fuska, ba ƙaramin abu ba ne zai sanya mijin nata hawaye. Tabbas za ta so jin yadda aka haihu a ragaya.

Zama ta gyara tana fuskantar sa ta ce, "Ka faɗa min abin da ke faruwa mana ka bar ni cikin duhu."

"Ba sabon abu zan faɗa miki a kan wanda ki ka sani ba game da Masarautar Joɗa. Hadiza, sai dai abin da zan faɗa miki yana buƙatar na fara tunatar da ke abin da ki ke da sanin shi."

Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi kafin ya ɗora dacewa.

"Masauratar Joɗa wacce ke wani babban gari a tsakiyar Arewacin Nijeriya, na da ƙabilu da addinai daban-daban waɗanda ke zaune a wannan gari cikin lumana. A can wani zamani da ya shuɗe, akasarin mutanen da ke cikin wannan gari sun maida hankalin su ne kacokam kan sana'o'in gargajiya irin su noma, saƙa, ƙira, kiwo, jima da sauransu.

"Sai dai shuɗewar shekaru da dama tare da wallafar wasu ababen zamani ya sa suka fara watsi da sana'o'in da aka san su da shi, suna mayar da hankali kana bin da zamani ya zo da shi.

"Ba shakka ilimi na taimakawa wajen gina
al'umma ta gari, dalilin da ya sa kenan Sarkin da ke mulkar wannan yanki a wannan lokacin ya tsaya kai da fata don tabbatar da cewa yara da matasa masu tasowa sun samu ingantaccen ilimin da zai amfani al'umma.

Ya numfasa kaɗan, sannan ya cigaba. "Kamar yadda aka ce makashinka na tare da kai hakan ce ta faru don kuwa wasu daga cikin amintattu da aka naɗa domin kawo cigaba a wannan yanki, suke ƙoƙarin warware kyakkyawar saƙar da ake yi domin inganta rayuwar al'umma. Koda yake sai bango ya tsage ƙadangare ke samun damar shiga.

"Yawaitar sace-sace da fashi da makami, sune suka yi silar da aka fara samun rashin jituwa tsakanin mutanen wannan yanki, cikin lokaci ƙanƙanin aka fara samun yawaitar rigingimu tsakanin ƙabilu da kuma addinai.

"Yayin da mutane suke tsaka da tashin hankalin fitinun da suka yi musu sarƙa,
a gefe guda kuma wasu da ke da hannu cikin abin da ke faruwa suna murna, ba ko waɗanne mutane ba ne face wasu daga cikin mutanen fada. Burin su shi ne a samu rashin zaman lafiya ta yadda Gwamnati za ta zargi Sarki da Shugaban ƙaramar hukuma inda za ta ɗauki mataki mai girma ta hanyar kare wannan muƙamai ta bai wa wasu daga cikin waɗanda suke son su da mulkin Masarautar Joɗa."

Cike da rauni ya kalli Hadiza da ke faman sharar kwalla ya ɗora da cewa.

"Matsayina a gidan Sarauta ba a iya
wanda ke bai wa dawakai abinci ya tsaya
ba, ina ɗaya daga cikin mutanen da Waziri Sarki ya naɗa domin raba wa matasa kayan maye tare da makamai cikin sirri. Yana ba mu kuɗi sosai hakan ya sa duk matasan suka watsar da karatun su da sana'o'in su suka mayar da hankali kan mugun aikin da ake saka su.

"Duka abubuwan da ke faruwa a wannan garin mu muke aikata su. Fashi da makami, satar mutane, kisan kai, tada rigimar tsakanin addinai da ƙabilu daban-daban da sauran abubuwa.

"A yanzu haka rikicin da ake yi tsakanin addinai guda biyu, mu ne muka haddasa shi ta hanyar kashewa kowanne ɓangare rayukan mutane dama, ta haka ne muke ɗar sa zargin juna a zukatansu. Akwai saka hannun wasu daga cikin jami'an Gwamnati saboda wani kaso da ake basu, shi ya sa ba a taɓa nasarar bayyana mu a matsayin masu aikata mugun laifi ba."

"Innalillahi Wa Inna ilaihirraji'un!
Ashe da ɗan ta'adda nake zaune ban sani ba."

Kuka ta fashe da shi tamkar wacce ta sa
mu saƙon mutuwar iyaye. Sun daɗe a wannan yanayin yana tausarta kafin ta nisa ta ce, "Ka je ka bayyana gaskiya tun kafin ranar tonuwar asirinku."

"Shawarar da na yanke kenan nima,
duk da na san zan fuskanci barazana sosai amma dole na tona asiri, bai kamata mu cigaba da zama a haka, rayukan al'umma na da tsada sosai, bai kamata a dinga kashe rayukan mutanen da ba su ji ba bare su gani."

Da wannan shawarar suka ƙare zancen, zuciyoyi sam babu daɗi musamman Naziru da yake tunanin ba zai tsira ba daga mugayen mutanen da yake ƙoƙarin tonawa asiri.

Washegari tun da jijjifi Naziru ya wuce
fada, a nan ya tarar da sabon jami'in da aka naɗa don jagorar tawagar kwantar da tarzoma. Bai ji mamaki ba yadda a lokaci guda zuciyar sa ta aminta da jami'in, tun da dama da mai kama ake yin ƙota, duba da yadda yake bayanai a kan hanyoyin da suke son bi don kawo ƙarshen matsalar da ake fuskanta. A sirrance ya samu damar keɓewa da shi ya bayyana mai abubuwan dake faruwa tare da lissafa sunayen duk waɗanda ke da hannu akan mugayen ayyukan da ke faruwa a yankin.

Kwatsam! Mutane na tsaka da harkokinsu,
sai ga motocin hukumomin tsaro fiye da
goma sun shigo cikin garin, kai tsaye kuma fadar Masarautar Joɗa suka nufa.

Ko da Sarki ya ji bayanan sirrin da aka gano, ba tare da ɓata lokaci ba ya ba da haɗin kai da goyon bayan ɗaukar dukkan matakin da ya kamata.

Nan take aka shiga zaƙulo mutanen da ake zargi. Duk wanda aka kama sai ya ambaci sunan mutanen da suke aiki tare. A haka har sunan waɗanda ba a yi tsammanin suna ciki ba ya fito. Bayan al'amura sun lafa ne Babban Jami'in rundunar tsaro ta ýan sanda mai kula da Masarautar Joɗa ASP Jibrin Adamu ya shirya taron masu ruwa da tsaki na yankin, shugabannin rundunonin tsaro, ýan banga da manema labarai, domin gabatar da mutanen da aka kama gaban jama'a.

ASP Jibrin ya miƙe gaban taro ya yi taƙaitaccen bayani yana mai cewa. "Ba iya haƙƙin Gwamnati ba ne tabbatar da tsaro da zaman lafiya a cikin al'umma. Hakkin mu ne baki ɗaya. Masu hikimar magana suna cewa, hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka.

 
"Matsalar tsaro ita ce hanyar samun kuɗin wasu da ke da alhakin tabbatar da tsaron.
Idan aka zauna lafiya ba za su samu kuɗin da suke so ba, saboda haka matsalar tsaro ta zama wa gwamnati gagara badau.

"A saboda haka ne ake amfani da matsalarmu wajen samun kuɗi, kuma idan ba a gyara wannan al'amari an yi maganin irin waɗannan baragurbin mutane ba, matsalolin mu ba za su ƙare ba. Mu da ya kamata a ce mun haɗa kuɗi da ƙarfi wajen gyara al'amuran tsaro da ke addaba mu a Arewa sai muka sauka kan waccan hanyar ya zamanto matsalar tamu ita ce cinikin mu.

"Shugaba, ko mabiyi, ɗan siyasa ko ɗan kasuwa, basarake ko jami'in gwamnati, attajiri ko talaka, kowa da kowa yana da rawar da zai iya taka wa wajen maganin matsalar tsaro da ke damun ƙasar nan, musamman yankin mu na Arewa.

"A binciken mu mun gano cewa, akwai jahilci da rashin aikin yi wanda ke taka muhimmiyar rawa kan matsalolin tsaro da muke samu. A lokacin da aka ce kowa yana da sana'ar da yake yi, masu ta da ƙayar baya ba za su yi nasarar ruɗar mu da ƴan kuɗaɗen da za mu yi amfani da su wajen tada tarzoma ba.

"Muna da sana'o'i da yawa da za su kawo mana kuɗi ba tare da mun jira aiki daga Gwamnati ba. Mu duba sana'ar noma wanda bahaushe ke wa laƙabi da na duƙe tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya tarar. Akwai ma wasu sana'o'in kamar Ƙira, Jima, Saƙa da Rini, sana'o'i ne da za su kawo mana cigaba sosai idan mun inganta su."

Ya kammala da cewa, "Lallai ne mu tashi tsaye don ganin cewa ba mu bai wa wasu mutane damar cusa ƙiyayyar juna a zuƙatan mu ba."

Daga haka aka sanar da jama'a da ýan jarida cewa za a gurfanar da waɗanda aka kama gaban kotu bayan an gama bincike, don a hukunta su, bisa laifukan da suka aikata na cin amanar ƙasa.

Tun bayan faruwar haka sai matasan Arewa suka dage wajen inganta sana'o'in su na gado a zamanance, tare da ƙara ƙaimi wajen neman ilimi don yaƙi da jahilci.

Hakan ya taimaka sosai saboda an rage samun yawaitar matsalolin tsaro da ake fama da su a yankunan Arewacin Najeriya.


ƘARSHE 

Reactions
Close Menu