TUN RAN GINI... LABARIN HAJARA AHMAD MAIDOYA

TUN RAN GINI... 

         Hajara Ahmad Maidoya (Oum Nass) 


GABATARWA

A shekarar 2021 da ta gabata ne ƙungiyar Arewa Media Writers reshen Jihar Filato ta shirya wata gasar marubuta ta Gajeren Labari da Insha'i ƙarƙashin jigon FARFAƊO DA KYAWAWAN AL'ADUN AREWA DON INGANTA TSARO DA ZAMAN LAFIYA, wanda ta kasance irin ta ta farko da wata ƙungiyar marubuta ta shirya a Jihar Filato, wacce ta ƙunshi marubuta maza da mata da suka fito daga sassan Nijeriya da ƙungiyoyin marubuta daban daban. Labarin TUN RAN GINI... na Hajara Ahmad Maidoya (Oum Nass) daga ƙungiyar Nagarta Writers Association da ke Haɗejia a Jihar Jigawa shi ne ya zo zakara a mataki na uku a gasar. Za mu ci gaba da kawo muku jerin sauran taurarin labaran da suka yi fice a gasar, don amfana da darussan da labaran ke koyarwa.

*****                        *****                       *****


Wani zafi nake ji yana huda fatar jikina
wadda ban taɓa jin irin sa ba a tsawon
rayuwata. Yayin da wasu manyan tsutsotsi
suka kewaya gangar jikina suna cizo na.
Hakan ya haddasa min ƙwalla ihu ina neman ceto. Sai dai babu inda sautin ya fita, hasalima kamar yana dawowa gareni ne.

Daga nan na hango wasu halittu baƙaƙe
masu firgitarwa suna ta jana da wani jan
sasari kai ka ce dalmar wuta ce don azaba,
suna nufar wani ƙaton rami da ni. Tun daga nesa na fara jin hucin wuta na tafasa naman jikina. Ina ƙara yin ihu ina neman ɗauki a inda babu wani mahaluƙi da zai ji ni. Har zuwa sanda suka jefa ni a cikin ƙaton ramin da ya ke cike da macijai da suke juye min zuwa suffar ƴaƴana, suna laso harshen su. Yayin da wutar da ta ke ruruwa ta ke dannasu zuwa ƙasa suna ƙara miƙewa da son kamo ni.

A firgice na farka daga barcin da nake
ina salati, gumi ya jiƙa ni sharkaf, kai ka ce na yi wasan tseren ruwa ne.

Da ƙyar na iya miƙa hannuna na kunna
fitilar ɗakin, haske ya gwauraye a kan
idanuwana, na fara yawata su a ɗakin da ya cika da kayan alatu na more rayuwa, daga
kan abin kallo zuwa na sauti.

A hankali na miƙe a kan ƙafafuwana na
shiga banɗaki na ɗauro alwala na daɗe ina tsaye ina neman yafiyar Ubangijina da kuma neman yarda a gare shi. A lokacin kuma tunani na ke wulla ni zuwa wasu shekaru.

****
Sunana Sulaiman Abdallah. Na kasance
ɗa na biyar ga mahaifina, ina da yayye maza biyu mata biyu.

Mahaifinmu ya kasance malamin
tsangaya ne, wadda ya ke koyar da yara
karatun allo. Yana da kyakkyawan mu'amala tsakaninsa da maƙotansa da ƴan uwansa. Duk satin duniya yakan sanya mu a gaba ni da yayyena mu kai wa ƴan uwansa ziyara. Idan mun yi laifi ko kuskure kaɗan
yakan tsawatar mana sosai, wani lokacin maƙwaftansa ma kan iya dukan mu idan mun yi abu ba daidai ba. Mu yaransa da na maƙwaftansa ya kan haɗa ya mana ɗinki da wani abu na alkhairi.

Har zuwa lokacin da na girma ya sa ni
makarantar boko, saboda bashi da ɗabi'a ta ƙin ilimin zamani gani yake kowanne ilimi ɗaya ne, amma kafin mu shiga ta zamani dole sai mun yi sauƙa mun kuma ci gaba da zuwa makarantar Islamiyya.

Zamani ya zo mana da abubuwan sauyi
na more rayuwa kama daga kan tauraron ɗan Adam har zuwa kan wayar salla. Amma duk da haka mahaifinmu bai bari mun mallaki ko abu guda ɗaya ba. Ba wai don bashi da kuɗin da zai siya ba, a'a yana gani dukkansu abubuwa ne da suke ruɗar da tunanin mutum da shagalar da shi.

Har zuwa lokacin da na ƙare karatuna na fito da kyakkyawan sakamako, babban
yayana da ya kasance ɗan kasuwa kuma ma'aikacin gwamnati ya min tayin aikin sa da kuma kasuwancin sa. Amma ni ba na sha'awar yin aiki a ƙarƙashin sa, domin rayuwar sa sak ta ke da ta mahaifinmu. Ba shi da lokacin fahimta da kuma sauraron abin zamani.

Bana manta wata rana ina zaune ina jin kiɗa da abin sautin kunne (Mp3) mahaifina ya same ni. Hankalin sa ya tashi ya cire abin ya
tattaka shi ya fara min faɗa "Sule, menene
abin sha'awa a wannan abin? Ashe ban
haneka da abin da zai shagalar da kai ba? Kiɗa a gidana?" Ya yi maganar cikin tashin
hankali.

"Ya za mu yi ne, Abba? Ka hana mu kallo,
ka hana mu riƙe waya, duk inda muka wuce abokanan mu na mana dariya suna mana
kallon ƴan ƙauye. Har gobe ba ka sauya ba, kullum muna tafe da ƙafafuwan mu don gaida ƴan uwanka, bayan ga waya nan ta zo mana  da ababen sauƙaƙa wahalar tafiyar mu. Ni na gaji."

Ina gama maganar na fice na bar gidan ina jin idanuwan mahaifina na yawo a kaina,
tun lokacin ya fita a lamura na yana kuma
bina da addu'ar shiriya.

Na samu aiki a wani kamfanin fata, na
dawo gida na shaidawa mahaifina ya bini da  fatan alkhairi ya kuma shaida min auren Karima ƴar maƙwafcinsa. Ban musa ba domin nasan a gidan mu aure ake mana. Bayan  aurena da Karima na samu ƴancin rayuwa. Na kafa tauraron ɗan Adam a gidana, na mallaki wayar zamani.

Duk wani abu na ƙyale-ƙyalen rayuwa
nakan mallake shi. Na manta cewa ni ɗan
Malam Audu ne. Duk da Karima bata da
wannan ra'ayin.

Har zuwa lokacin da muka hayayyafa na
haifi yara uku mace da maza guda biyu. Ban musu iyaka da mallakar duk wani abin jin daɗin rayuwa na zamani ba, duk
sanda suke buƙatar kuɗi nakan ba su ba tare  da tunanin mai za su yi da shi ba. Idan wani a cikin maƙwaftana ya musu faɗa ko ya dake su a kan wani kuskure na kan shiga maganar na fatattaki maƙwafcin nawa.

Mahaifina ya sha ja min kunne da ƴan
uwana amma ban ji shi ba, ƙarshe na yanke zumunci da ƴan uwana, na mayar da
rayuwata daga ni sai yarana sai kuma abin da suke so. Idan matata Karima ta yi musu faɗa na shiga tsakanin al'amarinta, ta hanyar mata kashedi a kan yarana.

Wata rana na ji babban ɗana yana waya
yana cewa "Oga, tsabobin sun faɗo." Ban ji
mai ogan ya ce ba ya yanke waya.

Tambayar sa na yi a kan mai yake
magana, ya ce "Ai sabuwar manhaja aka buɗe mana ta whatspp da muke aiki ake biyan mu. Muna zaune suka koyar da mu dabarun aikin." Ban bincika lamarin ba na yi gaba abina cike da alfahari.

*****                      ******                        *****


Kiran sallar Asuba ne ya tada ni daga
kan shimfiɗar sallah ta na tafi masallaci, a
lokacin na tadda mahaifina da ƴan uwana, da suka cika da mamakin ganina yau a masallaci ina sallah.

Na nemi yafiyarsu domin ni kaɗai na ga
abin da na gani a mafarkina. Allah ya nuna min ishara mai girma, Mahaifina mutumin
kirki ne ƙwarai, ya yafe min nan take ya kuma sa ƴan uwana su yafe min.

Da na dawo gida na ciccire kowanne
abin ƙawa na shagala na watsar da su, na
amshe wayoyin hannun yarana gaba ɗaya
hatta ta Karima sai da na karɓa na haɗa ta da wata mai tocilan a goshi. Ita ma saboda kiran nan take idan matsala ta biyo baya.

Na nemi yafiyar maƙwaftana a kan
kuskuren da na aikata a garesu. Na haɗa kan yarana na kai su wajen mahaifina, don ya koyar da su ilimin karatun addini.
Abin da ban sani ba na makaro da yawa
domin yarana sun bijirewa muradina. Suka gudu daga hannun mahaifina. Macen ce ta
zauna.

Na yi kuka mai yawa kamar raina zai fita,
ƴan uwana na bani baki. "Sule, ka fahimci abin da ake nufi da rayuwa a yanzu? Nasarar rayuwa ba tana nufin ka so naka ba ne. Kana ta ƙorafi a kan ina tursasa ku da yin wasu abubuwa da ba na addini ba ne, amma ko sau ɗaya ban tauye muku rayuwa an barku a baya ba. Na tsaya muku kun samu ilimi, na gina katanga mai ƙarfi tsakaninku da abubuwan da za su ruɗar da rayuwar ku dan kada ku manta asalin ku. Na ɗorar da ku akan kyakkyawar al'adarmu ta zama tare da hira tare. Na kuma ɗora haƙƙin kula da tarbiyarku ga maƙwaftana da kuma ƴan uwana idan bana nan. Amma kai me ka yi wa naka yaran? Ka basu cikekkiyar dama na samun ƴancin kai. Ka raba tsakanin su da al'adar su da addinin su, ka sa shamakin gyara tsakanin maƙwafta da ƴan uwanka. Har sai da suka girma suka saba  da rayuwar jin daɗi sannan ka yi tunanin za su gyaru da muradin ka? Ka makara domin
tun ran gini tun ran zane."

Kalaman mahaifina suka zama silar
gangarowar hawaye a idona, gaskiya ce da ya saba faɗa min ita wadda a baya nake ɗauka takura ce.

"Allah ya haɗa su da misalan ray..."

"Kul ka sake aikata wani kuskuren, Sule.
Ka nema musu shiriyar Allah da kyakkyawar rayuwa a inda za su. Domin nima ban ma baki ba a lokacin da ka bijire min."

Shuru na yi ina neman yafiya ga Allah,
na kuma ɗauki aniyar yiwa yarana addu'ar shiriya a duk inda suke. Bayan watanni shida, sai ga su kamar an jeho su dukansu sun fita a kamanninsu, sun shaida mana cewar suna fita suka gudu wajen ogan da na ji suna waya da shi, ashe mai garkuwa da mutane ne da ya ke amfani da asusun bankin su ana turo masa kuɗaɗen fansar yara. Sun koyar da su aiki a zauren WhatsApp da suka buɗe.

Ƴan sanda suka kama su suka kai su kurkuku, ganin su yara ne. Sauran aka kashe su.

Da kansu suka tafi wajen mahaifina
suka ɗauki allon karatu suka fara karatu.

Rayuwarmu ta miƙe ta hanyar ɗoruwa
da cigaba da bin al'adar gidanmu. Mun
fahimci al'adarmu na tafiya ne da tsarin da addinin mu ya koyar da mu.


ƘARSHE

Reactions
Close Menu