Kwamitin alƙalai sun bayyana marubuta 6 da suka yi nasara a gasar gajerun labaran powa

Kwamitin alƙalan gasar ƙungiyar Potiskum Writers Association wato POWA a takaice, sun fitar da sakamakon gasar kungiyar mai jigo akan "SIYASA 'YANCI". 

      Sanarwar sakamakon gasar wadda aka bayyana a shafin yanar gizo na ƙungiyar na ɗauke da hotunan takardun shaidar shiga gasar da marubutan suka yi tare kuma da matakan da labaransu suka kai na yin zarra a kakar gasar. 

Ga dai jerin sunayen marubutan da suka lashe gasar kamar yadda aka wallafa a shafin kungiyar;

1. Ahmad Ibn Umar

2. Kamal Muhammad Lawal

3. Muhammad Bala Garba

4. Binyamin Zakari Hamisu

5. Usman Mairiga Jega

6. Umar Usman Assafiy

A wannan mako ne ake sa ran kungiyar za ta saki jigon da za a fafata gasar watan Disamban da muke ciki wanda kuma shi ne gasar da za ta dauki nauyi na karshe a wannan shekara.


Close Menu