Littafin Daren Aurena (1)Na

Naanah M Sha'aban

Shafi Na 1

 

Kuka take tamkar ranta zai fita kwance take a kan d'an k'aramin gadon d'akin ta duk'unkune a cikin bargo ta rintse idonta zuciyarta nayi mata wani irin zafi da k'una cikin da sasshiyar muryarta ta fara magana "tabbas nayi dana sanin, sanin Jabir a rayuwata, ka cuceni, ka yaudareni bazan tab'a yafe maka ba har duniya ta nad'e, Insha...insha Allahu, Allah sai ya saka min abin da kayi min Kuma....." Sai Kuma ta kasa k'arasawa saboda irin kukan da ya shak'eta.

 

Aunty Murja ce ta shigo d'akin da sallama d'auke a bakinta zuciyarta cike take da tausayin k'anwarta ta saboda Jabir yabar mata mugun tab'o Wanda bazan tab'a gogewa a cikin zuciyarta da ma rayuwarta gaba d'aya, yayi mata abinda ba za ta tab'a mantawa ba a daren aurensu.

 

Zuwa tayi kusa da ita ta zauna tare da jawota jikinta suka k'ank'ame juna suna kuka, sun d'auki kusan mintuna biyar suna kukan Aunty Murja ta had'iye nata kukan domin ta samu ta rarrashi k'anwarta ta, Cikin muryar rarrashi ta fara magana "Khadijatullah nasan akwai zafi sosai a cikin zuciyarki, abin da Jabir yayi miki sai dai muce Allah ya saka miki domin kinsan mu ba wani arzik'i ne damu ba, barantana muce zamu kai shii k'ara kotu abi miki hakk'inki, Kuma ko min kai Jabir k'ara a zamanin nan na yanzu babu abinda za'ayi Masa saboda Yana da kud'i, Dan Allah Khadijatullah kiyi hakuri kinsan yawan kukan nan zai iya haifar miki da wata matsalar Ina tsoron kar in rasa ki kamar yadda muka rasa iyayanmu ke kad'ai nake kallo nake jin dad'i a cikin zuciyata" ta k'arasa maganar hawaye na zuba daga cikin idanuwanta.

 

Khadijatullah ta d'auki kusan mintuna goma tana kok'arin tayi magana Amman kukan da take ya hanata tayi dakyar ta samu ta sassaita kanta ta fara magana cikin sark'ewar muryar "Aunty Murja nasan bakya son kina ganina a cikin irin wannan yanayin, Amman Aunty Murja Ina ga ba zan tab'a daina kuka ba, zuciyata ba zata tab'a daina min zafi ba, saboda yanzu mun d'aura k'awance da tashin hankali, Aunty Murja wallahi ina ga bak'in cikin Jabir ne zai kasheni" wani sabon kukan ne ya kwace Mata Aunty Murja ta k'ara rumgumeta sosai a jikinta, Khadijatullah ta d'auki kusan mintuna biyar tana kukan kafin ta cigaba da magana 


"Aunty Murja wallahi na tsani Aure kuma na tsani maza, wallahi da za'a bani dama da sai na kashe duk wani namijin da yake duniyar nan tabbas na yarda da maganar hausawa da suke cewa namiji ba d'an goyo bane duk yadda ka Kai ga goya shi wata rana sai yayi maka abin da ba kayi tunanin zai yi maka ba, Kuma idan kaga namiji a rana karka sake kace zaka jawosa inuwa idan kuwa ka jawosa wata rana kai zai tura cikin ranar, Aunty Murja namiji yayi min abinda har abada ba zan manta dashi ba a DAREN AURENA". Duk tana kuka take maganar zuciyarta na cigaba da yi mata zafi.

 

Aunty Murja kuwa bata iya cewa komai ba, ta cigaba da rarrashin k'anwarta ta har ta samu baci b'arawo ya saceta hamdala Aunty Murja ta shiga yi a cikin zuciyarta domin ta samu yau Khadijatullah tayi bacci Wanda rabon da tayi bacci tun ranar DAREN AURENTA wanda yau kwana uku kenan.

 

'BANGAREN GIDANSU JABIR

 

Zaune yake a kan kujera wacce ake iya kwantar da ita a kwanta, a farfajiyar gidan ya saka shisha a gaba yana zuk'arta a hankali daga shi sai wani gajeran wando dan ko riga babu a jikinshi, fari ne tas wanda kana ganinshi za kasan balarabe ne, gashin kansa ya kwanta luf sai shek'i yake yi yana da manya_manyan idanuwa wad'anda farare ne tas, dogon hancinsa yayi matuk'ar dacewa da d'an k'aramin bakinsa, wayarsa wacce take gefensa ce ta shiga ruri hannunsa yasa ya d'auketa tare da duba screen d'in wayar ganin wanda yake kiran nashi Teemarh namo ya gani, wani gajeran murmushi yayi sannan cikin sanyayayyar muryarsa ya ce "yau akwai harka kenan" d'aga kiran yayi ba tare da ya ce komai ba, daga b'angaren Teemarh namo kuwa cikin shagwab'a ta fara yi magana "baby shine jiya ba ka zo club ba ina ta jiranka, kuma bayan kasan kwana biyu nayi missing d'inka sosai" ta k'arasa magana cikin nark'ar da murya, Jabir ya d'auki kusan mintuna biyar kafin ya ce "Am so sorry dear wallahi na d'an je wani guri ne kuma ban dawo da wuri ba". Cikin nuna tsantsar kishinta a fili ta ce "ina kaje? kodai kaje gurin wannan tsohuwar matar taka" wata iriyar dariya Jabir yayi wacce kana jii kasan ta tsantsar mugunta ce yana dariyar ya ce "haba dai ai wannan ta riga da tayi expired, please ki kwantar da hankalinki, ai yayinta ya riga da ya huce tuntuni" Murmushi teemarh namo tayi ta ce "to shikenan baby yanzu yau dai zaka zo ko? Kasan wallahi nayi missing d'inka sosai i miss your hug i miss you so so much" murmushi Jabir yayi ya ce "zan shigo da daddare yanzu ina d'an hutawa ne" yayi maganar kamar wanda ake yi masa dole "Ok to shikenan sai da daddaren ina nan ina jiranka"

"Ok" yayi maganar a takaice.

"i love you"

"thanks you dear" 

Daga nan kowannan su ya ajiye wayarsa Jabir ya cigaba da zuk'ar shishar.

 

'BANGAREN KHADIJATULLAHI

 

Ta d'auki kusan awa d'aya tana bacci a jikin Aunty Murja dan ita ma har baccin ya d'auketa kamar an tsikareta ta farka a gigice, irin yadda ta farka ne yasa Aunty Murja ita ma ta tashi ta rikota "Khadijatullahi meya faru"

Kallon Aunty Murja take hawaye na kok'arin zubowa daga idanuwanta "bakomai" tayi maganar cikin muryar kuka rumgumeta Aunty Murja tayi tana bubbuga mata bayanta tana cigaba da yi mata nasiha mai ratsa zuciya daga waje suka jii anyi sallama ana kok'arin shigowa d'akin..........................

 

Karshen shafi na daya!


Close Menu