Littafin Daren Aurena (2)

Na

Nanah M Sha'aban 

Shafi Na 2

"Assalamu alaikum" Mai shigowar ta fada tare da tura kofar dakin ta shiga, Murmushi Aunty Murja ta sakar mata tare da amsa Mata sallamar "Wa'alaikissalam Amatullahi"

"Ina wuni Aunty Murja" Amatullahi ta tsugunna har kasa cikin ladabi tana gaisar da Aunty Murjan

"Lafiya kalau ya kike"

"Lafiya alhamdulillah"

 

Sai kuma ta komar da dubanta kan Khadijatullah wacce tayi luf a jikin Aunty Murja.

"Kawata ba dai har yanzu kuka kike yi ba, haba Khadijatullah dubi yadda fuskarki ta koma idanuwanki duk sunyi cikiciki saboda kuka ya kamata kisan cewa wannan kaddara ce Allah ubangiji ya dora Mana, Kuma dukkan musulmi ya kamata ya rumgumi duk iriyar kaddarar da tazo Masa Mai kyau ce ko akasin haka".

 

Shuru kawai Khadijatullah tayi tana sauraronta tana sauke ajiyar zuciya idanuwanta na cigaba da zubar da hawaye, tabbas tasan su Aunty Murja ba zasu tab'a fahimtar irin tashin hankali, bala'i da masifar da take ciki ba, taya za'ayi a daketa Kuma a hanata kuka, bayan sun san irin cutar da Jabir yayi mata tana jin labarai a gidan t.v, kuma tana jin labarai iriiri wadanda maza suka yiwa matayensu na cin mutunci, Amman ita Bata tab'a jin labarin irin abin da Jabir yayi Mata a DAREN AURENSU ba, ta yaya za'ayi ta manta da wannan daren, wanda take kiransa da bakin dare domin ita DAREN AURENTA ya kasance Daren bakin cikinta, Wanda har yanzu take cikin bakin ciki.

 

Amatullahi ta saka hannunta a kan fuskar Khadijatullah tana goge Mata hawayenta,nan ita da Aunty Murja suka sakata a gaba suna yi Mata hira domin su samu ta hakura, ita dai kawai jinsu take Amman a wannan karon tayi kokarin hadiye kukanta domin ta fahimci kukanta Yana jefa masoyannata guda biyu cikin tashin hankali, Aunty Murja ce ta tashi ta dauko musu abincin da ta girka a wani dan karamin kwanon silba, ta dawo gurin da take ta zauna tare da bude kwanon shimkafa da Mai da yaji ce, "Kash! na manta ban dauko cokula ba" 

 

Amatullahi tayi murmushi "To Aunty Murja bari in dauko miki" mikewa tayi ta nufi inda kwandon kwanukansu yake wanda babu wani kayan kirki a cikinsa, ta dauko cokula guda biyu wadanda kana ganinsu zaka san sunyi mugun dadewa domin har sun fara lankwashewa, zama tayi tare da mikawa Aunty Murjan cokulan "Gashi Aunty Murja" cokali guda daya ta karb'a sannan ta ce "to matso sosai muci abincin" Da sauri Amatullahi ta girgiza kai domin abincin dake kwanon bama zai ishesu ita da Khadijatullah ba, saboda bashi da wani yawa "Kaii Aunty Murja Alhamdulillah wallahi sai da naci abinci sosai kafin in zo" sai kuma ta mikawa Khadijatullah cokalin tana fadar "gashi nan kici abincin" girgiza kai ta shiga yi alamar bata cin abincin, cikin daurewar fuska Aunty Murja take magana "wato abin da kike son ki tsira kenan rashin cin abinci, ai shikenan tunda haka kika zab'ar wa kanki" sai kuma ta fashe da kuka, cikin tashin hankali Khadijatullah ta karb'i cokalin hannun Amatullahi "Aunty Murja Dan Allah ki dena kuka zan ci" ta fada tare da saka cokalin a cikin abincin, shuru Aunty Murja tayi ita ma ta shiga cin abincin loma biyar Khadijatullah tayi ta ajiye cokalin, ta zame ta kwanta a kan yaloluwar katifar da take kan gadon ta rufe Ido domin Bata so Aunty Murja ta kara takura Mata taci abinci, Aunty Murja ma Bata ce Mata komai ba, Amatullahi kuwa mikewa tayi tare da cewa "to Aunty Murja zan tafi".

"Amatullahi yau tafiya da wuri haka" murmushi tayi ta ce "wallahi Aunty Murja zamu je Unguwa ne da Mama shine nace Bari inzo na ganku kafin mu tafi" Aunty Murja ta ce "Allah sarki Amatullahi to mun gode sosai" "Haba Aunty Murja bakomai ai" zagayawa tayi daidai saitin kan Khadijatullah ta shafa fuskar ta ta tana cewa "To kawata sai na sake dawowa gobe idan yau min dawo da wuri zan kara dawowa na ganku" Kai kawai ta daga mata, Amatullahi ta kara yiwa Aunty Murja sai anjima sannan ta fita daga gidan da saurinta, Aunty Murja ta tashi ta shiga gyara dakin daga nan ta dawo kan gadon ta kishim gida tana sauraron radio da ta kunna a wata matatciyar radio duk rayi ragaraga.

 

'BANGAREN GIDANSU JABIR

 

Shirye yake cikin wasu kananun kaya, kyau iya kyau ya gama yi, turarurrukan dake kan madubin dakinsa wanda kamar shagon kanti saboda yawansu, ya shiga fasawa a duk jikinsa saboda duk yawan turaren nan sai da ya bisu daya bayan daya yana fesasu a jikinsa, wani dan karamin kum ya dauka kirar dubai shi kanshi kum din abin tsayawa ka kalla ne, ya shiga taje kannasa da kum din a hankali tamkar wanda a kace dole sai ya taje kannasa, sai da ya dauki kusan awa daya yana shiryawa, sannan ya nufi hanyar fita daga dakin, ko kulle dakin bai yi ba haka ya nufi b'angaren Mami Yana taku dayadaya kamar wanda yake tsoron tafiyar, a haka har ya isa part din Mami to sallama bai yi ba haka ya tura kai cikin falon nata a zaune ya tarar da ita tana kallon wani film a zee word, da sauri ya karasa kusa da ita ya rumgumeta tare da yi Mata kiss a kumatunta.

 

Murmushi Mami tayi tare da shafa kansa "Wow my son you look so Masha Allah" Murmushi yayi tare da cewa "Thanks you Mum I really love you so much" Mami ta ce "Me too My son I love you so much" Mikewa tsaye yayi tare da cewa "Mami zan tafi club sai na dawo a chan zan kwana naga magriba tayi ana ta nema na akwai Abu Mai muhimmanci da zanyi me" yayi maganar cikin Yana yin shagwab'a "To sai ka dawo, Allah ya kaika lafiya, Amman goben ka dawo da wuri saboda Aliyu zai dawo daga dubai Kuma da wuri sai sauka" cikin yanayin farin ciki Jabir ya ce "Kaii dan uwana Aliyu Ashe dai zan kara ganinsa kaii kamar ma kar inje club din saboda naga dan uwana nayi ten year fa ban saka shi a idona ba".

 

Murmushi Mami tayi "Ai sai gobe zai dawo kaga bai kamata kaki zuwa club din ba saboda kace akwai abinda zakai Mai muhimmanci ai sai gobe zai dawo ai har ka dawo ma" cikin yanayin jin dadi ya ce "please Mami karku je daukoshi har sai na dawo" wani kayatatcen murmushi tayi ta ce "karka damu zamu jiraka" wani irin tsalle yayi sannan ya nufi kofar fita daga falon Yana fadar "Yawwah Mami nagode sosai" da murmushi ta bishi sannan ta cigaba da kallonta hankalinta kwance

 

Shi kuwa Jabir Yana fita kai tsaye wajen da aka tanada dan ajiye motoci ya nufa, ya shiga sabuwar motar da Abbansu ya Aiko Masa da ita, Mai gadi ya bude Masa gate ya fita da gudu daga gidan bai zame ko ina ba sai club, ai kuwa yana isa club din tun kafin ya fito daga mota aka saka masa ihu, Yana fitowa daga cikin motar zee namo tazo da gudunta ta rumgumeshi tana yi masa kiss ta ko ina a jikinsa, daukarta yayi cak dan daman shi ma a matse yake yazo club din ya huta da Zee domin yana jin dadin yarinyar sosai hotel din club din ya nufa da ita, ana fa guri ya kara hau tsinewa da ihu, shi kuwa Jabir bai bii ta kansu ba domin burinsa kawai ya samu ya biya bukatarsa da Zee din, dakin da aka basa ya shiga, ya ajiye zee din a kan gado, ya cire mata kayan jikinta daman ba wani kayan kirki bane a jikin nata rigar bacci ce wacce ko gwiwarta Bata Kai ba, Bata da hannu dan haka ya zama duka rabin kirjinta duk a waje suke. 

 

A nan ya shiga tsotsarta ta ko'ina tamkar ya samu wata alewa, Zee abin nema ya samu dan haka ta sakar Masa dukkanin jikinta Yana tsotsarsa, Anan dai sukai ta sheke ayarsu (ni kuwa 'yar mutanan zazzagawa nace Allah ya shiryeku Amin) sai wajen isha'i sannan ya sauka daga kan Zee din Amman ita Zee din sam Bata so haka ba, saboda bata gama dawowa daidai ba, toilet ya shiga da niyyar yin wanka, Zee ya mike ta shiga cikin toilet din, ta tarar da Jabir har ya fara yin wankan bayansa ta hau ta fara shafashi a hankali "Baby kasan fa baka gama dani ba, dan ni ban koshi ba".

 

Jabir dai shuru yayi domin ya rasa masifa irin ta Zee kullum idan yayi sex da ita duk irin dadewar da zai yi a kanta sai tayi Masa korafin Bata koshi ba, janyota yayi ta dawo gabansa Yana kallonta tana kallonsa tana wurga Masa wani shu'umin murmushi.

 

Jabir ya ce......................

 

Karshen shafi na biyu

Daga Alkalamin 'yar mutanan zazzagawa

 

 


Close Menu