Littafin 'Yar Wahala (3)


Na

Rukayyah Adam Mu'azBismillahir Rahmanir RaheemBayan fitarsu daga cikin falon Safna ta durkushe kusa da mahaifinta tana wani marayan kukan da yasa shima ya fashe da kukan "kiyi hakuri abisa hukuncin dana yanke akanki shine dai dai yin hakan domin nasan tabbas zaiyad bazai taba daga muki kafaba kinga da yazo yaci zarafinki gwanda ya aure ki in yaso duk abunda zaiyi dake cikin hakkin aurene !


kuma ubangiji yasoki domin a yadda ya fada bai taba yiwa mace wannan alfarmarba sai ke kinga sai kisani ubangiji yana tare dake kuma bazai taba bari ki wulakanta a gurinsu ba ,Basu daukeki a matsayinda zaki basu matsala ba ,da yardar Allah kece zaki zame musu Dan hakin daka raina shine zai tsone maka ido,kece zaki tsone musu ido su rasa yadda zasuyi dake but hakan bazata faruba sai kin zama jarima sannan ki rage yawan tsoronsa domin shima halittacene yinsa akai,kamarke !Haka yakasance yayi ta lallashinta har yaga ta daina kukan ta tashi ta dauko abincin da suka mata sunci tare ta tashi ta daura alwala ta tayar da sallah.Kashe gari da misalin karfe goma na safiya suna zaune a cikin wannan dakin da aka sakasu tana yankewa mahaifinta kunbar kafa wata ma'aikaciya a gidan ta shigo tana kiransu zuwa main falo domin su kadai ake jira.


cikin mutuwar jiki suka fito daga cikin dakin suna shiga falon idanuwansu suka sauka akan jalila watan Matar Malam Auwal Baban safna watan ,Watan shi yaga matarsa ita kuma taga Auntynsu cikin mamaki da firgici suka dubeta .


But ita kuwa dubansu tayi ta watsar cikin jinkai da takama tana shan shisha sai busar da hayakinda kamshinsa ya cika falon batare da kowa yayiwa kowa magana ba .Mal Auwalu kuka yasaka kamar karamin yaro yana kallon jalila da irin cin Amanar datayi masa a take yagene duk wani abu da hadin bakinta akayi shi watan da dangari akanci gari ,dole yayi mamaki sabida yadda suka bi komai daki daki kamar sun riga sun tama komai ashe akwai wacce ta shirya komai akansu ashe ba son Allah da Annabi take musu ba .


sautin voice dinta yaji a cikin kunnensa "kadena yimin kallon maci Amana domin kasan duk hakurina da kawar dakai ,Bazan taba ganin wannan kwangilar ta millon daya kyale ba domin ko kaine kasamu yinta zakayi ,kadauka zama nake a tinaninka wannan sanar da nakeyi ta cinikin kayan miya da ita nake ciyar daku dakai da yayanka sabida neman gafara koh? to kaga inda nake zuwa ina raba dare ina samun hamsin dari ina ciyarku da ilimantar da yaranka dan haka godiya ma yakamata kayiwa Alh ba butulci ba sabida ya jima yana ci dai da shayar dakai duk da nima musayar haja muke ni dashi but yafi sakina ku kwantar da hankali kuci arziki ku barshi mazauninsa in kuma talaucin akeso aci gaba da ci sai inga wanda zai ciyar daku !


kanada yara kyawawa kasaka a kasuwa kullum karinga breakfast da dinnar da kaza da fresh milk da sassanyan ruwan gora !


tsawa ya daka mata cikin dacin rai "ya isa haka macuciya azzallima ina dukiyata da kikace in baki wacce nasiyar da gidana da kango nabaki na zata ke mutuniyar arzikice ina take !


tashi tayi ta dubesa cikin rainin hankali "aika cinyeta tun tuni time din danake daka sakwara da cin indomie bani kai ?ai agabana nasaka muka cinyesu tass dan haka nayi ciki in kwanta in huta kafin in fita zagaya gari ,nan da one week mu dage Dubai !

suna kallonta tahau saman kai tsaye tayi bagaren dakin Alh Sayyid.Duk abunda suke Alh sayyid yana ji da ganinsu but baice kalaba time din data hau saman ,kallonsu yayi ya sake shuumin murmushin da shi kadai yasan ma'anarsa.


Time din wasu malamai ne su uku suka shigo kowa da ma Babbar rigarsa kowa da malim malim a jikinsa suka shigo da sallama suka zube a gaban Alh suna kwasar gaisuwa .


A cikin kankanin lokaci aka daura auran Zaiyad da Safna akan sadaki Dubu dari .


securityn gurin su suka cika da farin cikin da annushuwar goron da alawar da dabinon su aka rabawa kowa da malam suka tafi da nasu , ana daura auran da yan dakiku kadan ya fito daga bangarensa cikin rashin walwala sosai akan face dinsa .


sanye da wani mugun yadinda yake walkiya kamar madubi yasha wani irin cin bakin da gabaki dayan jikin akawa sai sheki gashin kansa yake kamshi kuwa turaren jikinsa tuni ka karade ilahirin falon sai jinsu duk najikin falon yake .yana sara saukowa da wata bakar leda a hannunsa wacce yake dagawa da kyau da kagani kasan kayane cikinta ,ya zube shanyayyun idanuwansa akanta yaki ko kiftawa yana raya abubuwa da yawa akanta har ya karaso gurin datake ya tsugguna ya dago kanta yasaka idanuwanta anashi wanda tin sanda taji kamshinshi ta sauri ta sunkuyar da kanta cikin tausayawa rayuwarta data mahaifnta domin karamar kanwarta Aminiyar mamanta da daukesu basama cikin garin .


hada idanuwa sukayi tai sauri ta kwace kanta ta saka masa kuka.


mikewa yayi cikin tsaki domin gani yake kukan da take yawan yi raina masa hankali tayi tunda shidai bai taba bayar da umarni kan karya masa ba sai ita ,sabida yana yiwa mutane mugun kwarjini but baisan mai yasa bayawa Baby Safna kwarjini ba ,wannan ne yasaka ta mugun rainasa.


Cikin isa da takama hade da gadara ya wulla mata kayan hannuns "kije ki canzasu zamu fita unguwa dake ,kuma kisani daga yau tsohonki ne drivern mu shine zai ringa kaimu duk inda muke so !

Sannan kisani ni ma,aboci kallo ne a cinima da zuwa casu clups ,zamu ringa zuwa ,drivern mune zai kaimu wani time din sai ketowar asba zan dawo !


wani zubin sai cikin dare zai jiramu har time din dazamu dawo sai yadawo damu ,in yaso sai ya fadi me za,a ringa bashi domin samun na cefani !


kuka tasaka tare da daukeshi da mari ,Dai dai nan Alh Sayyad ya shigo falon ai kuwa take ya dauke mahaifinta da marinda a take jini ya wanke masa hanci da baki.


Idan zaki daga hannu sau goma a jikin son wlh a jikin tsohonki zan rama masa ,domin shine rayuwarki ,nima shine tawa rayuwar !Dagowa yayi ,ga hannunta nan kwance a farar fuskarsa gurin yayi jajir .


Duban Malam Auwal yayi ,kamar babu abunda yafaru "me ka yanke akan salary dinka a shigar dakai cikin ma'aikata !


Cikin kuka,tare da durkushewa a gurin "Dan Allah Dan Alh kada ka cutar da ita na yadda ba sai da ko sisi ba idan zaka rikemin ita babu cutarwa !


cikin murmushi "yarinyar taka tana bukatar horo in domin rainita yayi yawa,kosai nayi mata kalar tawa a gabanka ne watan akuyanci inajin shine zai saka taringa respect dina oho but gaskiya saina horata horo mai girma domin abunda take yimin wlh babu mahalukin da ya taba mafarkin yimin irin hakan "


Da sauri ya juya gurinda Safna take cikin bacin rai da kumburarran bakinsa" indai nine mahaifinki duk abunda aka kuma yimin kika kuma magana ni Auwalu ban yafe muki ba ,kuma wlh tafiyata zanyi har abada bazaki kuma jin duriyata ba!


Tafi yakamayi yana murmushi " Bari muga kincika yar halak me jin maganar mahaifinta ,domin duk yar halak bazata juri ganin ana mazgar ubanta ba !


kuma kisani duk ranar da muka fita dashi a matsayin Driver yake a gurina don kada yayi min wani abun inyi masa wani abun kiji haushi domin now his my driver !!!Dan haka kije ki saka wadannan kayan kuma duk yadda sukai muki kada ki cire haka nakeson ganin Abubuwana kuma ki sani fita babu mayafi da duk da duk irin kayan dana dama koda kuwa da sleeping dress ne haka nayi niyya domin ko kadan bana kishinki ,hassalima inga ana rosh din surarki ,but babu halin tabawa !!!
shiga dakin tayi cikin bin umarnin mahaifinta domin taga yadda ransa ya gama baci ,katon madubine kato a ciki ta cire kayan taga doguwar rigace ita da babu duk daya gabaki dayan gaban rigar a waje sai wani net a jiki shima baro baro .


zare ido tayi tare da daga hannu ta dora aka tafasa ihu domin bata taba iya saka wannan kayan ta fita dasu baaaaaahhhhhh......MORE COMMENTS MORE TYPES....


GODIYA SOSAI DA GANIN COMMENTS DA SHARHI ,WLH BANYI ZATAN CEWAR NAN DA NAN BOOK DIN NAN ZAKU KARBESHI BA YAU WAJAN KIRAN MUTUM GOMA NA AMSA AKAN SUNA BUKATAR TYPES KUNSAKA MIN NIMA SON BOOK DIN ,SHA ALLAH ZAKU RINGA GANIN TYPES AKAN KARIIIIIIMUJE ZUW....

Close Menu