Subscribe Us

header ads

Yadda kalaman Umma Shehu suka tada ƙura a tsakanin mabiyanta

Daga Musaddam Idriss Musa

Jaruma Umma Shehu ɗaya ce daga jerin jarumai mata da kawo yanzu suka shafe shekaru suna kan cin ganiyar su a babbar masana'antar shirya finafinan Hausa da ake kira Kannywood inda har ta kai ga mallakar kamfani nata da take shirya finafinai mai suna 'Yar Shehu wanda kuma cibiyarsa ke a garinsu jarumar na haihuwa wato Kaduna. 

(Hakkin mallakar hoto) Jaruma Umma Shehu


 A wata hira da jarumar tayi da manema labarai cikin shirin Daga Bakin Mai Ita na BBC, Umma Shehun ta bayyana cewa, ko da a ce an titsiyeta bisa tuhumar yin gulmar wani ko wata a bayan idansu, hakan ba zai ɗaɗata da ƙasa ba domin a cewarta, ita sam ba ta shayin furta hakan ko da kuwa za ta fanjama fanjam saboda a wajen ta yin gulma ba wani abin kunya ba ne kuma ba abin tsoro ba ne, 


...ai ba cikin shege nayi ba da zan ji kunya, wallahi ba wani abin kunya a gulma." in ji jaruma Umma Shehun. 

● An taba min marin da sai da na ga wuta - in ji Shehu Hassan Kano

Jarumin fim a Kannywood yayi wa Gwamnan jahar Yobe takwara

 Sai dai da alamu kalaman nata bai yiwa jama'a da dama daɗi ba musamman masoyanta inda aka samu kaso mafi yawa na waɗanda suka bibiyi bidiyon hirar wanda shafin BBC din ya saka a 'yan wasu awanni da suka wuce na safiyar yau sun maida martanin da wasu daga ciki suka kasance kakkausa ga jarumar.  Sai dai kuma a wani ɓangaren kamfanin MTV arewa ya gargadin mutanen da suke sukar jarumar da cewa ko ma mene ne, ya kamata su kula suna kuma tuna cewa jarumar tana da haƙƙi akan su, 

 ku ji tsoron Allah ku daina aibanta wannan baiwar Allah. Ku sani sai Allah ya bi mata hakkin zaginta

in ji kamfanin MTV

Post a comment

1 Comments

  1. Ban ga laifinta ba dan ta fadi haka. Domin private mendevious dinta ne.

    ReplyDelete